Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin.

Cikin murmushi da annashuwa, Emefiele ya gaisa da shugaba Buhari a lokacin da shugaban kasa ke taya shi murna.

A cikin satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya sake aike wa da sunan Emefiele zuwa majalisa domin sake amince wa da shi a matsayin babban gwamnan CBN a karo na biyu.

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Buhari da Emefiele
Source: Twitter

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari
Source: Twitter

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Emefiele ya ziyarci Buhari
Source: Twitter

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Gwamnan CBN ya ziyarci Buhari
Source: Twitter

Ko a ranar Lahadi, sai da Legit.ng ta kawo muku labarin cewar ungiyar manoman Najeriya (AFAN) ta ce sake nada Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasa CBN da Buhari ya yi, ya kara tabbatar da niyyar shugaban kasa na inganta harkar noma.

Cif Daniel Okafor, mataimakin shugaban kungiyar, ne ya fada wa manema labarai hakan a Abuja yayin da yake yabon Buhari a kan sake nada Emefiele.

DUBA WANNAN: Matakai 5 da muka dauka domin magance matsalar tsaro a Najeriya - Fadar shugaban kasa

Okafor ya roki Emefiele da ya cigaba da bawa manoma tallafi a karkashin shirin nan na ABP a zango na biyu da zai shugabanci CBN.

Kazalika ya bukaci gwamnan babban bankin da ya duba yiwuwar kara yiwa manoma ragi a kan ribar da suke dora wa a kan kudin da aka basu rance, ta koma tsakanin kaso uku zuwa biyar.

Okafor ya yi kira na musamman ga Emefiele da ya kara kirkirar wasu shirin bawa manoma ttallafi da kara yawan kudaden da ake bawa bankin manoma (BoA) domin manoma su kara samun rance kudaden da zasu inganta sana'o'in su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel