Ba za a taba samun zaman lafiya ba a Najeriya har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa - Nwobodo

Ba za a taba samun zaman lafiya ba a Najeriya har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa - Nwobodo

- Sanata Jim Nwobodo yace Najeriya ba za ta taba samun zaman lafiya ba har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa

- Tsohon gwamnan na tsohuwar jihar Anambra ya yi furucin ne yayinda yake kira ga shugabancin Igbo a 2023

- Nwobodo yayi hasashen ne yayinda yake bikin cikarsa shekara 79 a Enugu

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Anambra, Sanata Jim Nwobodo yayi kira ga Shugabancin Igbo a 2023, cewa “Najeriya ba za ta taba samun zaman lafiya ba har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa.”

Nwobodo yayi hasashen ne yayinda yake bikin cikarsa shekara 79 wanda aka gudanar Enugu, jaridarVanguard ta ruwaito.

Ya kuma yi kira ga Ndigbo da su hada kai su mara wa duk wanda ke kokari domin ya wakilxi yan kin kudu maso gabas.

Ba za a taba samun zaman lafiya ba a Najeriya har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa - Nwobodo
Ba za a taba samun zaman lafiya ba a Najeriya har sai dan Igbo ya zama Shugaban kasa - Nwobodo
Asali: Facebook

Ya kuma yi kira ga bangaren shari’a da su isar da ayyukansu da adalci, cewa ta bangaren shari’a ne kadai za su iya ceto kasar daga durkushewa.

Ya jinjinawa gwamnan jihar Enugu, Hon. Ifeanyi Ugwuanyi, wanda ya bayyana cewa ya hada kan yan siyasa a jihar cikin aminci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zainab Aliyu ta iso gida Najeriya daga kasar Saudiyya, hotuna

Da yake Magana a taron, Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Chief Nnia Nwodo, ya bayyana Ugwuanyi a matsayin gwamna wanda shugabancinsa bai da iyaka.

Yace gwamnan baya tozarta kowa a cikin jam’iyyun siyasa saboda yana daukar kowa a matsayi guda.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel