An kaddamar da tashan sauke kaya a Kaduna

An kaddamar da tashan sauke kaya a Kaduna

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce tashar jirgin ruwa na kan tudu na Kaduna zai inganta tattalin arziki da kasuwanci a jihar Kaduna da Najeriya baki daya.

Ministan ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata a Kaduna wurin bikin fara sauke kaya da jirgin kasa ya kawo tashar na kan tudu.

Shugaban sashin ayyuka na ma'aikatan sufuri, Sani Galadanci ne ya wakilci ministan a wurin taron.

Ya kara da cewa jajircewar da gwamnati mai ci yanzu keyi wurin gyaran layyukan dogo da gina sabbi za suyi tasiri wurin inganta safarar kayayaki tsakanin sassan kasar.

An kaddamar da tashan jirgin ruwa na kan tudu a Kaduna

An kaddamar da tashan jirgin ruwa na kan tudu a Kaduna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa

A cewarsa, ma'aikatan sufuri da kungiyar masu safarar kayayaki ta jirgin ruwa na kasa ne suka bayar da goyon bayan wurin gina tashan domin magance matsalolin da ake fuskanta wurin jigilar kayayaki ta hanyar amfani da motocci.

Ya cigaba da cewa, "tashan jirgin zai rage tsadar kudin jigilar kaya kuma ya saukaka wa masu sana'ar jigilar domin tashan ya matso kusa da su."

Yayin da ya ke kira da masu ruwa da tsaki a fanin su hada kai wuri guda domin samun nasara, ya ce "tashan kuma zai habbaka tattalin arziki da cigaban al'umma."

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce tashan na kan tudu ya fara aiki kuma ya ce za a iya jigilar kaya daga kowanne kasa na duniya zuwa jihar Kaduna.

"Kaddamar da wannan tashar ya bude sabon shafi na kasuwanci ga 'yan kasuwan arewa da ma na kasashen da ke makwabtaka da Najeriya."

Ya ce tashan za ta samar da ayyuka ga dimbin al'umma tare da saukaka kasuwanci da noma ga 'yan arewa.

Gwamnan ya jadada cewa gwamnatinsa a shirye ta ke domin bayar da gudunmawa na tabbatar da samun nasarar tashan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel