Kungiyar kwadago ta yiwa Ministan kwadago kaca-kaca

Kungiyar kwadago ta yiwa Ministan kwadago kaca-kaca

Ministan kwadago na Najeriya Dakta Chris Ngige, ya bata bat yayin murnar bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a ranar 1 ga watan Mayun 2019 cikin harabar taro ta Eagle Square da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru aru-aru a tarihin Najeriya da Ministan kwadagon kasar zai kauracewa halartar bikin murnar ranar ma'aikata da aka saba gudanar wa a ranar 1 ga watan Mayun ko wace shekara bisa al'ada.

Shugaban kungiyar kwadago Ayuba Wabba tare da Ministan kwadago na kasa, Dakta Chris Ngige

Shugaban kungiyar kwadago Ayuba Wabba tare da Ministan kwadago na kasa, Dakta Chris Ngige
Source: Depositphotos

Sai dai ko shakka ba bu mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya halarci taron domin bayyana murnar sa tare da daukancin ma'aikatan Najeriya kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

A sakamakon kauracewa taron, kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta yi kaca-kaca da Dakta Chris Ngige, tare da misalta shi a matsayin daya daga cikin mayaudaran Ministocin Najeriya da suka shude a tarihi.

KARANTA KUMA: Masu garkuwa da Mutane sun yi awon gaba da Surukin Bafaden Buhari a garin Daura

Rahotanni sun bayyana cewa, mai magana da yawun Dakta Ngige, Nwakachukwu Obidiwe, ya bayar da shaidar cewa rashin wadatacciyar lafiya ta sanya uban gidan sa ya kauracewa taro yayin da ya ke ci gaba da 'yar gajeruwar jinya tun daga ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar kwadago da sanadin jagoranta na kasa, Mista Ayuba Wabba, ta fedewa Dakta Ngige Biri har wutsiya yayin da takun saka a tsakanin su ta tsananta biyo bayan takaddamar nadin Cif Frank Kokori, a matsayin shugaban kungiyar amintattu ta ma'aikatar ma'ajin inshorar zamantakewa NSTIF.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel