Majalisa: Masarautar Bade ta na so Goje da Ndume su bar wa Lawan takara

Majalisa: Masarautar Bade ta na so Goje da Ndume su bar wa Lawan takara

Masarautar Kasar Bade da ke jihar Yobe, tayi kira ga Sanatocin jam’iyyar APC Mohammed Ali Ndume da kuma Muhammad Danjuma Goje da su hakura su janye takarar da su ka fito a majalisar dattawa.

Wadannan Sanatoci su na harin kujerar shugaban majalisar dattawa a zaben bana, wannan ya sa wasu daga cikin masu sarauta a kasar Bade su ka roke su da su yi hakuri su marawa Abokin aikinsu watau Sanata Ahmad Lawan baya.

Alhaji Mamman Suleiman da Alhaji Mohammed Gagiyo ne su kayi magana a madadin Masarautar kasar Bade inda su kace akwai bukatar sauran manyan Sanatocin na APC su goyi bayan Ahmad Lawan domin a taimaki Arewa maso Gabas.

KU KARANTA: Sanatocin PDP za su marawa tafiyar Goje da Ekweremadu baya a Majalisa

Majalisa: Masarautar Bade ta na so Goje da Ndume su bar wa Lawan takara
Badawa su na so Goje da Ndume su hakura da takarar Majalisa
Asali: UGC

Mamman Suleiman yace abin da ya dace da Sanata Ali Ndume da kuma Danjuma Goje, shi ne su yi biyayya ga matakin da jam’iyyarsu ta APC mai mulki tayi na zaben Ahmad Lawan a matsayin wanda zai rike kujerar shugaban majalisa.

Masarautar ta ke cewa babu dalilin juyawa Ahmad Lawan baya, ganin irin tarin shekarun da yayi a majalisar tarayya. Har wa yau, Masarautar tace bai kamata a samu sabani tsakanin Sanatocin na ta da su ka fito daga Arewa ta Gabas ba.

Suleiman yake cewa an ta samun ta-ta-bur-za tsakanin fadar shugaban kasa da Majalisa a wa’adin farko na gwamnatin nan don haka ya nemi sauran ‘yan majalisar da su ba Sanata Ahmad Lawan hadin kai wajen ganin ya rike majalisar kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel