Yadda na koyawa Sanata Kwankwaso siyasa a kasar nan

Yadda na koyawa Sanata Kwankwaso siyasa a kasar nan

- Wani Kwamishina a jihar Kano ya bugi kirji ya yi ikirarin cewa shine wanda ya wayarwa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kai a siyasar kasar nan

- Ya ce ya sha bakar wahala kafin ya shawo kan Sanata Kwankwaso ya shiga harkar siyasa

Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi ikirarin cewa shine wanda ya fara shigo da tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya na yanzu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso siyasa a kasar nan, duk da cewa ya nuna ba haka abin ya ke ba.

Iliyasu ya shaidawa manema labarai hakan jiya a Kano, inda ya ce ya cancanci a dinga kiranshi da ubangidan Sanata Kwankwaso a siyasa.

Yadda na koyawa Sanata Kwankwaso siyasa a kasar nan
Yadda na koyawa Sanata Kwankwaso siyasa a kasar nan
Asali: UGC

Kwamishinan wanda ya bayyana irin hanyoyin da ya bi har ya samu ya ci nasara wurin shawo kan Sanata Kwankwaso cikin harkar siyasa, ya ce ya sha wahala sosai wurin shawo kan Sanatan, inda sai daga baya Sanatan ya amince da barin aikin gwamnati ya shiga harkar siyasa.

"Lokacin da na shiga harkar siyasa a karamar hukumar Madobi, lokacin da kuma na yi shugaban matasa na karamar hukumar, na san duk yadda harkar siyasa ta ke tafiya a wancan lokacin, kuma a lokacin ne na shigo da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso harkar siyasa, lokacin mutane da dama a garinmu ba su san shi ba.

KU KARANTA: Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta

"A lokacin saboda manya da na ke da su a harkar siyasa, sai muka saka shi ya fito takarar dan majalisar wakilai, kuma cikin ikon Allah sai ya lashe zaben."

Yayin da yake magana game da zaben da ya gabata, ya ce, "ko a lokacin zaben da aka gudanar, Kwankwaso ya kawo daruruwan 'yan daba daga Kaduna da sauran wurare domin su tada hargitsi a yi magudin zabe, amma cikin ikon Allah hakan bai faru ba."

Don nuna masa cewa har yanzu mu iyayenshi ne a siyasa, mun kada shi a karamar hukumar sa Madobi kuma mun kada shi a kauyensa Kwankwaso, inda Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya lashe dukkanin garuruwan na shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel