'Yan gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga a jihar Katsina

'Yan gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga a jihar Katsina

- 'Yan kauyen unguwar Bello da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina sun nuna jarumtar su a fili, a lokacin da suka yi fito na fito da masu garkuwa da mutane da suka kai hari kauyen

- Sun samu nasarar kashe daya daga cikin 'yan bindigar bayan sun yi mishi taron dangi a kauyen

Mazauna unguwar Bello da ke karamar hukumar Kafur cikin jihar Katsina sunyi nasarar dakile wani hari da masu garkuwa suka kawo garin, inda ake zargin sun zo sace wani ne a garin, a kokarin dakile shirin 'yan ta'addar sun samu nasarar kashe daya daga cikin masu satar mutanen.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina SP Gambo Isah shine ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru jiya Talata 23 ga watan Afrilun shekarar 2019.

Katsina: 'Yan gari sun dakile harin masu garkuwa da mutane, inda suka samu nasarar kashe daya daga cikin su

Katsina: 'Yan gari sun dakile harin masu garkuwa da mutane, inda suka samu nasarar kashe daya daga cikin su
Source: Depositphotos

SP ya ce barayin mutanen sun shiga yankin, inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi, amma mazauna yankin sun dakile harin na su. Ko da ya ke har yanzu ba a bayyana wanda aka kashe daga cikin barayin mutanen ba.

A cewarsa, "yau da misalin karfe 2 na dare, yan bindigar suka yi wa garin tsinke inda suka dinga harbi babu kakkautawa, sai dai kuma mutanen kauyen sunyi kokari sun dakile harbe-harben 'yan ta'addar.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba

"Mutanen garin sun yiwa daya daga cikin 'yan bindigar taron dangi inda suka kashe shi kafin jami'an 'yan sanda su iso garin.

"Amma jami'an 'yan sandan sun dauki gawar shi zuwa babban asibitin karamar hukumar Kafur," in ji SP Isah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel