Alkali ya daure wasu Matan Musulmai 2 da suka yi shigar banza a garin Kaduna

Alkali ya daure wasu Matan Musulmai 2 da suka yi shigar banza a garin Kaduna

Wata kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari cikin garin jahar Kaduna ta yanke ma wasu yan mata biyu, Farida Taofiq mai shekaru 20 da Raihana Abbas mai shekaru 20 ita ma, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 2.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, Mallam Musa Sa’ad Goma ya kama yan matan biyu mazauna layin Argungun ne da laifin yin shigar banza a matsayinsu na Musulmai, sa’annan suma matan da kansu sun amsa laifinsu.

KU KARANTA: Rikicin kabilanci: Mayakan rundunar Sojan kasa sun halaka Sojojin wata kabila a Benuwe

Da fari dai, lauya mai shigar da kara, Aliyu Ibrahim ne ya bayyana ma kotu cewa a ranar 16 ga watan Afrilu aka kama Raihana da Farida a wani waje da ake aikin badala a unguwar Sabon Tasha, sanye da kayan banza.

“Da aka tambayesu ina zasu je, sai suka ce zasu tafi gidan wata kawarsu ce data haihu don yi mata barka.” Inji lauya Aliyu Ibrahim. Lauyan ya kara da cewa laifin ya saba ma sashi na 346 na kundin dokokin shari’ar Musulunci na jahar Kaduna.

Suma yan matan sun amsa laifinsu, sa’annan sun nemi kotu tayi musu sassauci, suka kara da daukan alkawarin ba zasu sake aikata irin wannan laifi ba, sun tuba, kum sun yi nadamar abinda suka aikata.

Daga karshe Alkali Musa ya tuhumi yan matan da laifin sanya kaya masu nuna tsirai, da kuma tayar da hankalin jama’a, don haka ya yanke musu hukuncin zaman gidan Kurkuku tsawon watanni 2, amma ya basu zabin biyan taran naira dubu uku uku, sa’annan ya umarce kowannensu ta koma gidan iyayenta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel