An hana yar shahararren mai watsa shirye-shiryen talbijin shiga dakin jarrabawar JAMB, an nemi ta cire hijabi

An hana yar shahararren mai watsa shirye-shiryen talbijin shiga dakin jarrabawar JAMB, an nemi ta cire hijabi

Shahararren mai watsa shirye-shirye a gidan talbijin Sulamah Aledeh ya koka a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, cewa an hana yarsa shiga dakin jarrabawar UTME wanda aka fara a yau, Alhamis, 11 ga watan Afrilu.

A cewar Aledeh, an bukaci yarsa da tax ire hijabi kafi a bari ta shiga cikin dakin jarrabawar.

Cibiyar UTME din yana a New Ocean School, Megida, Ayobo.

Daga bisani Aledeh ya bayyana cewa an zo an bari yarinyar ta shiga jarrabawar bayan wasu yan mintuna. Don haka, yayi tambaya kan dalilin da zai sa ace mai rubuta jarrabawa ta cire hijabinta kafin shiga dakin jarrabawa.

Binciken Legit.ng ya nuna cewa hijabi baya daga cikin jerin abubuwan da JAMB ta haramta.

A bisa ga hukumar jarrabawar, an haramta wa dalibai miliyan 1.8 da za su rubuta jarrabawar UTME na 2019 kawo wasu kayayyaki 18 wajen jarrabawar.

KU KARANTA KUMA: Batan N38bn: Yan majalisar wakilai sun sanya manyan jami’an PenCom a kwana na tsawon sama da sa’o’i 3

Kayayyakin da ukumar JAMB ta haramta sun hada da, agogon hannu, biro da fensir, wayar hannu ko kuma kayayyakin wuta, gilashin ido na leken asirin karatu, na’urar lissafi da makamantansu, USB, CD, litattafai da duk wani abu na rubutu ko karatu.

Sauran kayayyakin da aka haramta sun hada da kamara, abun rikoddin, abun jin sauti, inki, zobuna/ kayan kyale-kyale, Bluetooth, katin ATM da abun goge rubutu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel