Dalilin da ya sa Burundi ta haramtawa Muryar Amurka da BBC aiki a kasar

Dalilin da ya sa Burundi ta haramtawa Muryar Amurka da BBC aiki a kasar

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Burundi ta haramtawa kamfanonin labarai na BBC da muryar Amurka daukar rahotanni a kasar, hukuncin da kafofin watsa labarai na duniya ke kallo a matsayin cin fuska ga 'yancin jarida.

Hukumar kula da kafofin watsa labarai ta Afrika ta tsakiya ta lalata lasisin aikin BBC da kuma zarginta da yada labarin da ta ce na karya ne wanda kuma cin fuska ne ga mutuncin kasar.

KARANTA WANNAN: Ziyarar kungiyar CAN fadar shugaban kasa ta bar baya da kura

Haka zalika ta kara wa'adin dakatarwar da ta yiwa kamfanin watsa labarai na Muryar Amurka, inda ta zarge ta da daukar ma'aikacin da ke adawa da gwamnatin.

Tun bayan watanni shida da suka gabata, Muryar Amurka da BBC suka daina watsa shirye shiryensu a kasar, bayan da kasar ta zarge su da karya dokokin aikin jarida da kuma nuna son kai a ciki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel