Rikicin APC a Zamfara: Gwamna Yari ya yiwa Allah laifi - Sanata Marafa

Rikicin APC a Zamfara: Gwamna Yari ya yiwa Allah laifi - Sanata Marafa

Sanatan jihar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa, ya bayyana cewar gwamna Abdulaziz Yari na jihar ta Zamfara ya saba wa Allah a kan hakikicewar da yake yi a kan cewar jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fidda 'yan takara a Zamfara.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan harkokin siyasa a jihar Zamfara, Sanata Marafa ya bayyana cewar kamata ya yi gwamna Yari ya nemi yafiyar Allah a kan yaudarar da ya yiwa mutanen jihar Zamafara a kan batun zaben fidda 'yan takara.

Kazalika, ya yaba wa kotun daukaka kara a kan hukuncin da ta yanke a kan karar da ya shigar dangane da batun rashin gudanar da zaben fidda 'yan takara a jihar Zamafara a jam'iyyar APC, ya bayyana cewar ya fitar da ran samun adalci bayan kotun wata kotun jihar Zamfara ta yanke hukuncin farko a kan karar.

Rikicin APC a Zamfara: Gwamna Yari ya yiwa Allah laifi - Sanata Marafa
Sanata Marafa
Asali: Twitter

A ranar 25 ga watan Maris ne kotun daukaka kara ta soke zaben fidda 'yan takara da tsagin da ke wa gwamna Yari biyayya su ka gudanar bayan kotun farko ta yanke hukuncin amince wa da zaben.

DUBA WANNAN: Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara

"Allah ne da kan sa ya yi alkawarin cewar ba zai bawa rashin adalci nasara a kan adalci ba. Ni na san Allahn da muke bauta wa ba zai bar wannan rashin adalci ba, shi dama hukuncin Allah daga karshe yake zuwa.

"Adalci daga karshe yake zuwa, ko ku nan sai a karshen wata ake biyan ku albashi ba a farkon wata ba," a cewar Sanata Marafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel