Yadda kananan yara masu talla ke yada cutar Kanjamau a Borno

Yadda kananan yara masu talla ke yada cutar Kanjamau a Borno

Rahotani sun nuna cewa akwai wani adadin 'yan mata masu dauke da cutar HIV mai karya garkuwar jiki da suke yawo a titunan jihar Borno suna talla kuma suna yada cutar ga abokan huldansu da ba su kame kansu.

Wani babban dalilin da ya ke kara yaduwar cutar na HIV/AIDs a jihar Borno shine dakatar da shirin daukan nauyin aure tsakanin mutane masu dauke da cutar domin a takaita yaduwar ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa 'yan matan da ke dauke da kwayar cutar ta HIV 'ya'yan zaurawa 4000 ne masu dauke da cutar da suka rasa mazajensu sakamakon ta'addancin kungiyar Boko Haram.

Zaurawan 4000 da 'ya'yan su mata suna daga cikin mutane masu dauke da su kayi rajista da kungiyar mutane masu dauke da kwayar cutar HIV/AIDS wato Network of People Living with HIV/AIDS (NEPWHAN) na jihar Borno a 2015.

DUBA WANNAN: Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

Yadda kananan yara masu talla ke yada cutar Kanjamau
Yadda kananan yara masu talla ke yada cutar Kanjamau
Asali: Twitter

"Wadannan zaurawan 4000 da 'ya'yansu mata ba su da 'yan uwa da za su taimaka musu da baya ga dan kankanin tallafin da suke samu daga SEMA da NEMA, wahalhalun rayuwa ke tilasta su sanya yaransu tafiya talla kuma daga nan 'ya'yansu ke yada cutar ga mazaje da ke basu kame kansu," a cewar jagoran NEPHWAN na Borno da Arewa maso Gabas, Hassan Mustapha.

A kasa muna murnar raguwar yaduwar cutar kanjamu amma a jihar Borno har yanzu ba a kai matsayin fara murna ba.

Ya ce hakan na faruwa ne saboda an gaza zartar da yarjejeniyar samarwa masu dauke da cutar bukatunsu uku a jihar.

"Yarjejeniyar ita ce, kula da bayar da tallafi; samar da magunguna da sinadaren abinci da koyar da sana'o'i. Wannan nauyin ya rataya ne a kan gwamnatin jihar Borno da masu bayar da gudunmawa kamar Bankin Duniya, FHI da UNFPA.

"Yarjejeniyar itace gwamnati za ta samar da kudi yayin da masu bayar da gudunmawar za su samar da magunguna, abinci da kuma koyar da sana'o'i."

Sai dai anyi korafin cewa gwamnatin bata biya kudin da ake binta ba har na tsawon shekaru uku wanda hakan yasa abokan huldar ta ke ja da baya.

Kwamishinan Lafiya na jihar Borno, Dr Salisu Kwaya ya ce bai san cewa gwamnatin ba ta biya na ta kason kudin ba.

"Ba ni da masaniya cewa gwamnatin jiha ba ta biya kason ta ba, amma zan bincika in gani.

"Na san cewa a cikin shekaru uku da suka gabata an samu karin adadin magungunan da ake sayowa domin masu dauke da cutar na HIV/AIDS," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel