Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayar da umurnin gaggauta mayar da hotunan Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sanusi II da aka cire a wasu wurare a jihar

- Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan jam'iyyar APC ne suka rika cire hotunan Sarkin a yayin da suke murnar lashe zabe a jihar bisa wata zargi da suke masa

- Gwamna Ganduje ya ce Sarki Muhammadu Sanusi II uban kasa ne jihar Kano ke alfahari da shi ba kuma ba zai bari wani abu ya lalata kyakyawar alakar da ke tsakaninsu ba

Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati
Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati
Asali: Twitter

Mun samu rahoton cewa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayar da umurnin gaggauta mayar da hotunnan mai martaba Sarkon Kano, Mallam Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi II da wasu matasa suka cire a dakin taro na nadin sarauta a Kano.

Legit.ng ta ruwaito cewa wasu matasa ne suka cire hoton Sarki Sanusi inda suke zarginsa na goyon bayan jam'iyyar adawa ta PDP a yayin zaben gwamna da ta gabata a jihar.

DUBA WANNAN: Zaben Kano: CUPP za ta garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Ganduje

Bidiyon yadda matasan suka rika yage hoton tuni ya karade shafukan sada zumunta na zamani.

Gwamna Ganduje ya ce, "Mun samu labarin cewa wasu magoya baya sun cire hotunan mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a lokacin da suke gudanar da shagalin zabe a dalilin wani abu da suka zargi game da shi.

"Don haka muna bayar da umurnin a dena cire hotunan kuma a gaggauta mayar da duk hotunan da aka cire a duk wuraren da aka cire su saboda mai martaba Sarki Uban kasa ne kuma muna alfahari da shi a wannan jihar.

"Ba za mu bari wani abu ya lalata dangantaka da kyakyawar fahimta da ke tsakanin mu da shi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel