Sarkakken lamari: Yadda dan sanda ya kashe wani jami'in Civil Defence

Sarkakken lamari: Yadda dan sanda ya kashe wani jami'in Civil Defence

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa wani jami’in dan sandan Najeriya da ba a bayyana ba ya harbi wani jami’in tsaro na Civil Defence har lahira a Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Maris.

An tabbatar da mutuwar jami’in Civil defence din mai suna Ogar Ochigbo a asibitin da ke Asokoro, Abuja inda aka garzaya da shi bayan afkuwar lamarin.

Majiyarmu ta bayyana cewa dan sandan ya farma jami’in Civil defense din ne bayan ya kama shi yana bin hanyar da bai kamata ya bi ba da mota.

Sarkakken lamari: Yadda dan sanda ya kashe wani jami'in Civil Defence
Sarkakken lamari: Yadda dan sanda ya kashe wani jami'in Civil Defence
Asali: Twitter

Jaridar Guardian ta rahoto cewa a lokacin da suke musayar yawu ne dan sandan ya harbi Ochigo.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Musulmai a unguwar Aleluya da ke Osogbo, babbar birnin jihar Osun sun shad a kyar yayinda wasu yan bindiga suka far masu da safen nan a hanyarsu ta zuwa masallaci.

KU KARANTA KUMA: APC za ta yanke hukunci akan yankunan da za su samu manyan mukamai a majalisa a mako mai zuwa

Musulmai a yankin sun bayyana cewa wasu mutane dauke da bindigogi sun far masu sannan suka yi kokarin bude masu wuta a hanyarsu ta zuwa masallaci domin sallatar Subuhi.

Mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar, Mista Abu Mustapha wanda ya ji labarin afkuwar lamarin ya tura yan sanda daga yankin Dada Estate.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel