INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano

INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano bayan takaddamar hargitsi da rudani da ta fuskanta da sanyin safiyar yau ta Litinin a karamar hukumar Nasarawa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar INEC ta dakatar da sanarwa da kuma tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano biyo bayan rudani da wasu kusoshin gwamnati suka haifar a karamar hukumar Nasarawa ta jihar.

INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano
INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano
Asali: UGC

Ko shakka ba bu hukumar INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 43 cikin 44 na jihar Kano, inda Abba Kabir Yusuf, dan takarar kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP ke kan gaba ta fuskar nasara sama da dan takara na jam'iyyar APC, gwamna Abdullahi Ganduje.

A halin yanzu dan takarar jam'iyyar PDP ya samu gamayyar kuri'u 960,004 yayin da Gwamna Ganduje ya samu kuri'u 953,522 bayan da hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 43 cikin 44 na jihar Kano.

A yayin da ake ci gaba a kirdadon sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa da ta ke cikin tantagwaryar birnin jihar Kano, babban Baturen zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu, ya kwantar da hankalin al'umma tare da bayar da tabbacin bayyana sakamakon zaben a yau Litinin.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Hukumar 'yan sandan jihar Kano na ci gaba da tsare kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule Garo, biyo bayan kekketa sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa da ya yi cikin duhun dare na jiya Lahadi.

Yayin ganawa da manema labarai na BBC Hausa, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakil, ya ce za a gurfanar da Murtala Garo gaban Kuliya da zarar hukumar sa ta kammala gudanar binciken ta na diddigi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel