Baya-ba-zane: Sabbin sanatocin da suka ci zabe 11 na rigima da kotu kan tafka sata

Baya-ba-zane: Sabbin sanatocin da suka ci zabe 11 na rigima da kotu kan tafka sata

Yayin da ake cikin shaukin sabukan da aka gudanar a dukkan kasa ranar Asabar din da ta gabata inda wasu suka samu nasara, wasu kuma suka ga akasin hakan, mun dan karkata kadan wajen zabukan da aka gudanar na 'yan majalisar dattawan kasar.

A wani duba na tsanaki da wakilan mu suka yi sun gano cewa akalla sabbin 'yan majalisun dattawan akalla 11 ne yanzu haka ke gaban kotuna daban daban suna shari'a kan zargin wawure dukiyar al'ummar su a baya.

Baya-ba-zane: Sabbin sanatocin da suka ci zabe 11 na rigima da kotu kan tafka sata
Baya-ba-zane: Sabbin sanatocin da suka ci zabe 11 na rigima da kotu kan tafka sata
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rarara ya saki sabuwar wakar nasarar Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan dai babban abun tsoro ne musamman ma ganin yadda ake son tsarkake majalisar daga dukkan bata-gari da 'yan siyasa marasa gaskiya.

Ga dai jerin sunayen Sanatocin da ake tuhuma a kotu:

1. Chimaroke Nnamani: Ana tuhumar sa ne da badakalar Naira biliyan 5.3 lokacin yana Gwamnan jihar Enugu.

2. Ifeanyi Ubah: Ana zargin sa da yiwa gwamnati karya wajen karbar kudade ba bisa ka'ida ba da suka kai Naira biliyan 43 na tallafi.

3. Orji Uzor Kalu: Ana zargin sa da wawure Naira biliyan 7.7 na dukiyar al'umma sadda yana gwamnan jihar Abia.

4. Gabriel Suswam: Ana zargin sa ne da aikata laifuka 32 da suka kunshe cinye kudaden talakawa har Naira biliyan 9.79.

5. Abba Moro: Ana tuhumar sa ne da shiryawa matasa gadar zare tare da yin sanadiyyar mutuwar su yayin wata jarabawar daukar aiki a shekarar 2014. Kuma ana zargin sa da cinye kudaden rijistar matasan.

6. Peter Nwaoboshi: Shima dai ana zargin sa da badakalar Naira miliyan 322 tare da hadin bakin wasu kamfanoni 2.

7. Stella Oduah: Ana zargin ta ne da cinye Naira biliyan 3.9 daga cikin Naira biliyan 9.4 na kudaden kwangilar gyaran filayen jiragen saman Najeriya.

8. Aliyu Wamakko: Tsohon gwamnan jihar Sokoto ne kuma ana zargin sa ne da sace Naira biliyan 15 ta dukiyar al'umma sadda yana gwamna.

9. Ike Ekweremadu: Ana zargin sa da mallakar kadarorin da suka wuce samun sa da kuma wawure kudaden talakawa.

10. Danjuma Goje: Tsohon gwamnan Gombe, EFCC na tuhumar sa da sace Naira biliyan 25 ta dukiyar talakawa.

11. Abdullahi Adamu: Yanzu haka yana fuskantar tuhuma kan laifuka 149.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel