Cikakken jawabin da Buhari ya yi bayan INEC ta sanar da nasarar daya samu

Cikakken jawabin da Buhari ya yi bayan INEC ta sanar da nasarar daya samu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabin farko tun bayan da hukumar INEC ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa daya gudana a ranar 23 ga watan Feburairu, inda ya bayyana godiyarsa ga Allah tare da miliyoyin yan Najeriya da suka bashi goyon baya.

Legit.ng ta ruwaito a daren Laraba ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

KU KARANTA: Shikenan: Buhari ya lashe zaben 2019, ya samu kuri'u 15,191,847

Cikakken jawabin da Buhari ya yi bayan INEC ta sanar da nasarar daya samu
Buhari
Asali: Twitter

A jawabinsa nasa da yayi da sanyin safiyar Larabar nan, Buhari ya gode ma Allah daya baiwa yan Najeriya ikon ganin wannan lokaci da aka samu cigaba a Dimukradiyyar kasa, da kuma nasarar da jam’iyyar APC ta samu.

2- “Na gode ma miliyoyin yan Najeriya da suka sake zabena a matsayin shugaban kasarku na tsawon shekaru hudu masu zuwa, ina kaskantar da kaina tare da gode muku da kuka ga dacewar zabata na cigaba da yi muku hidima

3- “Ina mika gadiyata ga Asiwaju Ahmad Bola Tinubu da rawar daya taka a matsayinsa na shugaban kwamitin yakin neman zabena, da shugaban jam’iyyarmu Adams Oshiomole, daraktan yakin neman zabe Rotimi Amaechi da sauran mambobin kwamitin.

4- “Ina kara jaddada godiyata ga wadanda suka taimaka mana da harkokin sufuri da zirga zirga har muka karade dukkanin sassan kasar nan a yakin neman zaben da muka yi.

5- “Ina kuma gode ma miliyoyin yan sa kai da duk wadanda suka bamu gudunmuwa a wannan yakin zabe da muka yi bisa sadaukar da lokacinsu da suka yi don ganin mun samu nasara, bani da isassun kalaman godiya a gareku.

6- “Duk da dai anyi zaben cikin kwanciyar hankali, amma wasu miyagu sun yi kokarin tayar da hankula a wasu jihohi, amma jami’an tsaro zasu tabbata an hukunta duk wadanda suka kama daga cikinsu.

7- “Na yi bakin ciki matuka da asaran rayukan da aka samu yayin zabukan, amma jami’an tsaro zasu kara zage damtse wajen ganin sun kare rayuka da dukiyoyin jama’a a zaben gwamnoni dake tafe

8- “Ina yaba ma jami’an tsaro bisa rawar da suka taka waken tabbatar da tsaron kasar a yayin zabe duk kuwa da cewa aikin yayi musu yawa.

9- “Ina kira ga masoya da magoya bayana dasu kada su ci fuskar abokan hamayya ko muzguna musu, nasarar da muka samu kadai ta isa sakayyar kokarin da muka yi.

10- “Mun gode ma masu sa ido akan zabe daga ciki da wajen kasarnan, musammab duba da gudunmuwar da suka bamu wajen tabbatar da nasarar zaben.

11- “Gwamnatinmu zata mayar da hankali game da matsalar tsaro, sauya fasalin tattalijn arzikin kasa, da yaki da rashawa. Mun shimfida tubali mai karfi, kuma zamu tabbata mun kammala duk aikin da muka fara, zamu tafi da kowanne bangare a gwamnatinmu.

12- “Nagode muku da goyon bayan da kuka bani, da fatan Allah Ya albarkanci kasarmu Najeriya.” Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel