Dandalin Kannywood: Yan daba sun kai ma Saratu Gidado farmaki har gida

Dandalin Kannywood: Yan daba sun kai ma Saratu Gidado farmaki har gida

Da alama ayyukan yan daba da masu zauna gari banza na neman sake farfadowa a jahar Kano, musamman ma a birnin Kano, tun bayan shigar kakar zaben 2019, domin kuwa a yan kwanakin da suka gabata an samu rahotanni daban daban akan ayyukan yan daba a Kano.

Anan ma wasu gungun yan daba dauke da muggan makamai ne suka kai farmaki gidan shahararriyar jarumar fina finan Hausa da aka fi sani da suna Kannywood, Saratu Gidado mai inkiya da suna Daso.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojin Najeriya sun sake samun gagarumar nasara a Madagali

Dandalin Kannywood: Yan daba sun kai ma Saratu Gidado farmaki har gida

Daso a kofar gida
Source: UGC

Legit.ng ta ruwaito Daso da kanta ta bayyana haka a shafinta na Instagram a ranar Laraba, 13 ga watan Feburairu, inda tace yan daban sun yi ma gidanta da na makwabcinta barna ta hanyar jifa da duwatsu da amfani da sanduna.

Wannan lamari dai ya faru ne a cikin daren Litinin, 11 ga watan Feburairu, sai dai jarumar tace yan daban basu kai ga shiga gidajen nasu ba sai jami’an Yansanda suka garzayo layin nasu.

“ Innalillah wa Inna ilaihi Raji'uuuuun…..yan daba suka zo Gidana dana Makocina suka yiwa Gidajen namu Rotse da Duwatsu da Sanduna suna Jifa har cikin Gidan mu.Sun kona Generator da wasu kayayyaki a Kofar Gidan namu.

“Sun lalata mana Dukiya me yawa, amman Allah be basu sa'ar Shiga Gidan namu ba Police suka zo. Masoya aci gaba da tayamu da Addu'a” kamar yadda Saratu Gidado Daso ta bayyana.

A wani labarin kuma da yammacin ranar Lahadi ne wasu miyagun fusatattun matasa suka kai farmaki zuwa wani gida mallakin dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Abba Kabir Yusuf, inda suka kone gidan kurmus.

Shi dai wannan gida yana nan ne a unguwar Chiranchi, kuma majiyar Legit.ng ta ruwaito Abba Yusuf ya gina wannan gida ne domin gudanar da tarukan siyasa, da na bukukuwa a cikinsa, a takaice dai jama’a ke amfani da gidan fiye da shi.

Idan za’a tuna mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya yi muhimmin gargadi da jagororin siyasar Kano da ma yaransu da kada su kuskura su jefa jahar Kano cikin fitintinun siyasa kawai saboda neman wasu bukatunsu na siyasa.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake ganawa da manema labaru a fadarsa dake cikin birnin Kano, inda ya bayyana matsayin masarautar Kano game da farfadowar ayyukan yan barandan siyasa a garin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel