Da dumin sa: Atiku ya dira a jihar Kano, hotuna

Da dumin sa: Atiku ya dira a jihar Kano, hotuna

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da tawagar yakin neman zaben sa sun dira jihar Kano.

Tuni dai sanarwa ta fita cewar Atiku zai ziyarci jihar Kano a ranar Lahada, 10 ga watan Fabariri, domin kaddamar da yakin neman zaben sa a jihar.

A ranar Larabar makon jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddanar da kamfen din sa a jihar Kano.

Da dumin sa: Atiku ya dira a jihar Kano, hotuna

Atiku ya dira a jihar Kano
Source: Twitter

Da dumin sa: Atiku ya dira a jihar Kano, hotuna

Atiku ya dira a jihar Kano
Source: Twitter

Da dumin sa: Atiku ya dira a jihar Kano, hotuna

Atiku ya dira a jihar Kano
Source: Twitter

Atiku tare da darektan kwamitin yakin neman zaben sa, Bukola Saraki da ragowar 'yan tawagar kamfen din sa da shugabannin jam'iyyar PDP, sun samu tarba daga jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

DUBA WANNAN: Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

An samu barkewar cece-kuce gabanin ziyarar ta Atiku bayan gwamnatin jihar Kano ta yi yunkurin hana Atiku filin taro. Sai dai, daga baya gwamnatin ta yi mi'ara koma baya, ta bawa Atiku damar yin taron kamfen din sa a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata a cikin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel