An kama wani mutum da ke danne yaro dan shekara 13 ta dubura
- Yan sanda sun cafke wani mutum da laifin danne wani yaro mai shekaru 13 ta dubura
- A dalilin wannan ta'asar da ake yiwa yaron ya kamu da cutar kanjamau
- Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Imohimi Edgal ya ce a mika Prince kotu da zarar sun kammala bincike
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wani mutum da aka ambata da suna Prince Chinecherem da laifin danne wani yaro mai shekaru 13 ta dubura.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imohimi Edgal ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Edgal ya ce a dalilin wannan abu da Prince yake yi da wannan yaro, ya sanya yaran kamuwa da cutar nan mai karya garkuwar jikin dan Adam wato kanjamau.
“Wannan abin takaicin ya faru ne a Ejigbo ranar 22 ga watan Janairu.
“A Wannan ranar makwabtan Prince ne suka kama wannan yaro yayin da yake sanda yana kokarin ya gudu.
“Da suka damke shi sai suka tambaye shi me ya kai shi dakin Prince. Sannan suka bude wani bakar leda dake hannun sa sai suka ga kwaroro roba ne da aka riga aka yi amfani da su da dama a ciki."
KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalili da yasa Oshiomhole da Amaechi ba sa farin ciki da ni – Okorocha
Edgal ya ce bayan an kawo Prince da wannan yaro ofishin su ne aka yi musu gwaji a asibiti.
Ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa an dade ana lalata da wannan yaro ta baya sannan dukkansu na dauke da cutar kanjamau.
Edgal ya ce za a mika Prince kotu da zarar sun kammala bincike.
A wani lamari na daban, mun ji cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisar jihar Katsina Bello Abdu Danmusa da yar sa.
Hajiya Amina Danmusa ta auri wani mai suna Miftahu Yakubu Ciro a garin danmusa inda a nan ne lamarin ya afku.
Wadanda lamarin ya afku a gabansu sun bayyana cewa masu garkuwar sun kawo farmaki ne a kokarin su nayin garkuwa da mijinta amma saiya kasance bayanan.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng