Rashin doka da tsari ya sanya ake fataucin Matan Najeriya zuwa kasar Saudiyya

Rashin doka da tsari ya sanya ake fataucin Matan Najeriya zuwa kasar Saudiyya

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, wasu miyagun ababe da rikon sakainar kashi na gwamnatin tarayya na ci gaba da taka rawar gani tare da kasancewa musababbin fataucin Matan Najeriya zuwa kasar Saudiya.

Rashin ingatattun tsare-tsare da dokoki na ma'aikatar kwadago da aikace-aikace ta Najeriya na da tasirin gaske wajen ci gaba da fataucin Matan Najeriya zuwa kasar Saudiya da sunan fita cirani.

Rahotanni kwanaki kadan da suka gabata sun bayyana cewa, da taimakon ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Saudiya aka samu nasarar dawo da kimanin Mata 1000 'yan asalin kasar nan da suke faman aikatau da yiwa Larabawan Saudiya hidima a gidajen su.

Binciken da manema labarai suka gudanar ya bayyana cewa, garin neman gira ya kan sa a rasa idanu ya tabbata kan wadannan Mata da suke samun lasisin shiga kasar Saudiya domin aikatau na tsawon shekaru biyu bisa ga taimakon ma'aikatar kwadago ta gwamnatin tarayya.

Shugaba Buhari tare da Sarki Salman na kasar Saudiyya

Shugaba Buhari tare da Sarki Salman na kasar Saudiyya
Source: UGC

Lamarin da a halin yanzu ya sanya da dama daga cikin Matan suka shaidawa manema labari halin cuzguni da suka fuskanta yayin zaman su a kasa mai tsarki kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Baya ga kwadago na aikatau ba bu kakkautawa, mafi akasarin Matan bayan fuskantar cuzguni na Uwar gijiyoyin su da ke danganta su a matsayin bayi, su na kuma fuskantar barazana ta keta haddi da cin zarafi na fyade musamman daga bangaren Mazajen da ke gidajen su na aikatau.

Daya cikin wadanda garin neman gira ta rasa idanun ta 'yar asalin jihar Kaduna, Ladidi Danliti, ta zayyana yadda ta karfin tsiya wasu Mazaje uku suka rika tsallaka ta karo bayan karo a gidan da ta ke aikatau baya ga cin zarafi da wulakantaswa da ta fuskanta wurin uwar gijiyar ta.

Ladadi a madadin ta shafe tsawon shekaru biyu tana aikatau kamar yadda yarjejeniya tayi tanadi, ta nemi dawowa kasar ta ta gado bayan wata guda kacal sakamakon mummunan bala'in da ta rika fuskanta.

KARANTA KUMA: Buhari ya sayar da tashar jirgin Gwamnati ga 'Yan kasuwa akan N105bn

Takaitattun rahotanni sun bayyana cewa, Ladidi bayan shafe wata guda ta tsira da Riyal 950 da suka yi daidai da Naira 92,313 a kudin Najeriya a madadin Naira 250,000 na ladan aikatau da ya kamata ta samu a kowane wata.

Duk da sa hannu da kuma yarjewar gwamnatin tarayya, hukumomin tsaro na kasar nan sun shaidawa manema labarai cewa akwai wasu ababen na fatauci da cin zarafin bil Adama a wannan lamari.

Bugu da kari binciken ya tabbatar da cewa, baya ga 'yan kasar Najeriya, akwai kuma 'yan kasashen nahiyyar Asia da ke fuskantar wannan ibtala'i a hannun Larabawan Saudiya da suke ma su hidima da aikatau musamman 'yan kasar Indonesia da Phillipines.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel