Ikon Allah: Wata yarinya da aka haifa da kafafu da hannaye hudu ta cika shekaru 2, hotuna

Ikon Allah: Wata yarinya da aka haifa da kafafu da hannaye hudu ta cika shekaru 2, hotuna

- Yarinyar da aka haifa a kasar Indiya da hannaye hudu da kafafu hudu ta cika shekaru 2 a duniya

- Har yanzu yarinyar tana cikin koshin lafiya kuma iyayenta basu da niyyar yi mata tiyata domin rage hannu da kafafuwarta

- Mutanen kauyen suna girmama yarinyar sosai inda suke mata kallon wata abin bautar hindu mai suna Vishnu

Shekaru biyu da suka wuce ne aka haifi wata yarinya Lakshmi Tatma a hannaye hudu da kafafu hudu a kasar India. Haihuwarta ya bawa mutane mamaki sosai har ta kai wasu mutanen suke ganin abin bautarsu mai suna Vishnu ne ta sake dawowa duniya.

Sai dai ainihin abinda ya faru shine Lakshmi yar uwanta 'yan biyu ne tun a cikin mahaifiyarsu amma kafin a haife su sai aka samu matsala da cikin dalilin hakan jikin 'yar uwar Lakshmi ya shanye amma hannayenta da kafafunta suka hade da jikin Lakshmi.

Ikon Allah: Wata yarinya da aka haifa da kafafu da hannaye hudu ta cika shekaru 2, hotuna

Ikon Allah: Wata yarinya da aka haifa da kafafu da hannaye hudu ta cika shekaru 2, hotuna
Source: Twitter

Amma wannan bai hana mutanen Indiya yi mata kallon Alliya Vishnu ba wadda dama tana da hannaye hudu ne da kafafu hudu kamar yadda masu addinin hindu ke gina gunkinta.

Ikon Allah: Wata yarinya da aka haifa da kafafu da hannaye hudu ta cika shekaru 2, hotuna

Ikon Allah: Wata yarinya da aka haifa da kafafu da hannaye hudu ta cika shekaru 2, hotuna
Source: Twitter

Iyayaen Lakshmi sun ce mutanen kauyen su suna daraja ta sosai.

A shekarar 2007, an taba haihuwan wata yarinya itama da hannaye hudu da kafafu hudu a garin Bihar na Indiya amma daga bisani likitoci sunyi mata tiyata an cire kafafu da hannu biyu.

Kamar Lakshmi, itama mutanen kauyensu sun dauke ta a matsayin Alliyarsu ta Hindu.

Wasu masu wasanin kayatar da mutane sunyi kokarin daukarta haya amma iyayenta basu amince ba hakan yasa suka bukaci likitoci suyi mata tiyatan. Anyi tiyatan ne a asibitin Bangalore kuma an samu nasarar kammalawa lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel