Mataimakin gwamnan jahar Kano ya yi ram da fitaccen dan jagaliyan siyasa a Kano

Mataimakin gwamnan jahar Kano ya yi ram da fitaccen dan jagaliyan siyasa a Kano

Shahararren dan jagaliyan siyasan nan mai yi ma kansa kirarin ’Jagoran Ummati’, wato Mustapha Jarfa ya fada komar rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kano a ranar Laraba 2 ga watan Janairu.

Legit.com ta ruwaito wannan kame na Jarfa bata rasa nasaba da wani bidiyo daya fitar a watan Disambar data gabata, inda a cikinsa aka jiyoshi yana cuccusa ma mataimakin gwamnan jahar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna manya manyan zagi, har ma yace idan ya isa kada ya bari ya kwana.

KU KARANTA: Atiku ya zargi Buhari da danniya tare da cin zalin yan adawa

Mataimakin gwamnan jahar Kano ya yi ram da fitaccen dan jagaliyan siyasa a Kano

Jarfa
Source: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewa yaran siyasan gidan Gawuna ne da kansu suka fita farautar Jarfa, inda suka yi masa a tara tara a lokacin da suka yi arba da shi, daga nan suka mikashi ga ofishin Yansanda na karamar hukumar Nassarawa dake unguwar Gwagwarwa.

Shi dai wannan bidiyo da ake tuhumar Jarfa akansa ya wallafa shi ne a shafinsa na Fesbuk, wanda yace yayi shi ne a gaban ofishin daya kafa na yakin neman zaben dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Abba K Yusuf, bayan nan kuma ya sake sakin wani sabon bidiyo akan Gawuna ya tura an lalata ofishin.

Mataimakin gwamnan jahar Kano ya yi ram da fitaccen dan jagaliyan siyasa a Kano

Jarfa
Source: Facebook

Mustapha Jarfa matashin dan siyasa ne daya shahara wajen harkar jagaliyar siyasa, kuma ya karade jihohin Kano, Jigawa da Kaduna yana tallata hajarsa, inda yan siyasa da dama ke janyoshi a jiki domin ya tallatasu a gidajen rediyo, musamman filayen shirin siyasa.

Amma kamar yadda yake fada da kansa, wannan sana’a tashi ta sha jefa shi cikin ruwan zafi, inda mutane daban daban musamman yan siyasa suka shigar da kararsa sau goma sha daya gaban kotu.

Hatta wakilin Legit.com ya taba sauraran wani daga cikin hukuncin da aka taba yanke masa a lokacin da dan majalisar wakilai mai wakiltar Nassarawa ya shigar da shi kara gaban kotu akan yayi masa kazafi, inda Alkali ya yanke masa hukuncin bulalai da dama, wakilinmu na ji aka dinga shauda masa bulalan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel