Najeriya ce a mataki na 110 cikin jerin kasashen duniya mafi kyawun kasuwanci - Forbes

Najeriya ce a mataki na 110 cikin jerin kasashen duniya mafi kyawun kasuwanci - Forbes

Duba da nazari kan adadin al'umma da kuma kyawun tattalin arziki, fitacciyar mujallar nan ta Forbes mai rataye da akala ta gudanar da kididdigar al'amurra daban-daban da suka shafi duniya, mun kawo muku jerin kasashen duniya mafi kyawu ta fuskar kasuwanci.

Najeriya ce a mataki na 110 cikin jerin kasashen duniya mafi kyawun kasuwanci - Forbes
Najeriya ce a mataki na 110 cikin jerin kasashen duniya mafi kyawun kasuwanci - Forbes
Asali: Facebook

Cikin wannan kididdiga da mujallar Forbes ta fitar, Najeriya ta kasance kasa da ta ke mataki na 110 cikin kasashe 161 na duniya da aka gudanar da kididdigar a kansu.

Kasar Afirka ta Kudu ta kasance a mataki na farko cikin jerin kasashen nahiyyar Afirka, inda Najeriya ta ke mataki na 14 cikin kasashen da ke makwabtaka da ita.

Kasashe 10 da suka yi zarra da fintinkau a fadin duniya dangane da kyawun harkokin kasuwanci sun hadar da;

1. Birtaniya

2. Sweden

3. Honk Kong

4. Holland

5. New Zealand

6. Canada

7. Denmark

8. Singapore

9. Australia

10. Switzerland

Jamus ce kasa da take mataki na 14 yayin da kasar Amurka ta ke a mataki na 17 karkashin kasar Ireland da kuma Finland.

Kasashen nahiyyar Afirka da ke cikin wannan kididdi tareda matakin su sun hadar da;

Afirka ta Kudu (59)

Morocco (62)

Seychelles (66)

Tunisia (82)

Botswana (83)

Rwanda (90)

Kenya (93)

Ghana (94)

Masar (95)

Namibia (96)

Senagal (100)

Zambia (103)

Cape Verde (104)

KARANTA KUMA: Dakaru sun fi mayakan Boko Haram nagartattun Makamai - Hukumar Sojin Kasa

Wannan kididdiga ta yi daidai da kudiri na majalisar dinkin duniya, cibiyar tattalin arziki da kuma bankin duniya.

A bara Najeriya ta kasance a mataki na 115 cikin jerin kasashe duniya 153 da aka gudanar da kididdiga a kansu, inda ta kasance a mataki na 15 cikin jerin kasashen nahiyyar Afirka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel