Allah-gamu-gareka: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane 18 a jihar Zamfara

Allah-gamu-gareka: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane 18 a jihar Zamfara

Akalla mutane 18 ne wasu 'yan bindigar da ba kai ga sanin ko suwaye ba suka kashe lokacin da suka kai hari a wasu garuruwa biyu na jihar Zamfara dake a Arewa maso yammacin Najeriya dake ke fama da tashe-tashen hankula a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekarar nan.

Majiyar mu ta Premium Times dai ta tabbatar mana da cewa garuruwan da suka samu cewa an kai harin sune Dutsin Kure da kuma Manasa dake a cikin karamar hukumar Tsafe.

Allah-gamu-gareka: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane 18 a jihar Zamfara

Allah-gamu-gareka: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane 18 a jihar Zamfara
Source: Twitter

KU KARANTA: Dan majalsar Tarayyar Najeriya ya rasu

Legit.ng Hausa ta samu cewa mutane 9 ne 'yan bindigar suka kashe a kauyen na Dutsin kure haka zalika ma mutane 9 suka kashe a garin na Manasa tare kuma da barin wasu da dama da munanan raunuka.

A wani labarin kuma, rundunar Sojojin Najeriya sun fara aikin kwashe mutanen garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa a jihar, zuwa tuddan mun tsira don tseratar da su daga yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojin Najeriyar da mayakan Boko Haram a yankin.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ ta fitar dauke da sa hannun mataimakin kakakin ta, Kanal Onyema Nwachukwu a ranar Lahadi, rundunar sojin Najeriyar ta ce matakin zai ba dakarunta damar yakar mayakan Boko Haram din a duk inda suke a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel