Kisan Janar Alkali da Badeh: Akwai lauje a cikin nadi - Rahoton kungiyar Amurka

Kisan Janar Alkali da Badeh: Akwai lauje a cikin nadi - Rahoton kungiyar Amurka

Wata kungiya ( International Strategic Studies Association (ISSA) ) mai cibaya a birnin Washington na kasar Amurka ta ce kisan Janar Idris Alkali da na tsohon shugaban rundunar sojin sama, Alex Badeh, ba tsautsayi ba ne, shiryayyen abu ne.

Ana zargin wasu gungun matasa 'yan kabilar Berom da kashe Janar Idris Alkali a garin Jos a ranar 3 ga watan Satumba, yayin da wasu 'yan bindiga suka bude wa motar Alex Badeh wuta a hanyar Abuja zuwa Keffi ranar 18 ga watan Disamba.

ISSA, kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta dake bincike da nazari a kan harkokin tsaro, ta ce an kashe manyan sojojin biyu ne domin boye wani salon cin hanci da rashawa dake faruwa a shugabancin rundunar soji ta Najeriya.

A rahoton da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an kashe Badeh don kar ya bayar da wasu muhimman bayanai a kan irin cin hancin dake faruwa a shugabancin rundunar sojin Najeriya na yanzu.

Kisan Janar Alkali da Badeh: Akwai lauje a cikin nadi - Rahoton kungiyar Amurka

Janar Alkali da Badeh
Source: Twitter

Kungiyar ta kara da cewa akwai rahoto da aka mika wa Buhari a kan badakalar sayen makamai a hukumar soji wanda har yanzu ya ki bayyana wa kowa duk da kwamitin da ya kafa ya mika masa rahoton fiye da shekara guda da ta wuce.

A cewar kungiyar, manyan shugabannin rundunar soji na kasa, sama, da na ruwa sun dade suna amfani da rashin tsaron Najeriya wajen azurta kansu daga makudan kudaden da gwamnati ke warewa a harkar tsaro.

DUBA WANNAN: Wasu sabbin sojoji sun tarwatsa taron biki, sun ci mutuncin jama'a haka siddan

"Manyan shugabannin rundunar soji da hukumomin tsaro sun shiga tashin hankali tun bayan da kwamitin da shugaban kasa ya kafa ya mika masa rahoto. Hakan ya saka su tashi tsaye wajen kokarin ganin sun kawar da duk wata kafa da shugaban kasa zai samu rahoto a kan yadda shugabannin ke kulla almundahana da sunan sayen makamai," a cewar rahoton.

Sannan ya cigaba da cewa mayar da hankali da shugabannin rundunar soji suka yi a kan rufe kofofin fitar da bayanai a kan badakalar sayen makamai ne ta jawo har mayakan kungiyar Boko Haram suka kara samun karfi har suke kara tsananta kai hare-hare a kwanakin baya bayan nan.

"Yanzu haka jami'an leken asiri na Najeriya da ma'aikatan tsaro na farin kaya basu san da wacce kungiya ake yaki ba, basu san wadanna kungiyoyi ne yanzu ke yaki da gwamnati da sunan Boko Haram ba," a cewar rahoton.

Rahoton ya ce duk rashin zaman lafiya da ake fama da shi arewacin Najeriya yana da alaka da cin hanci dake gudana a shugabancin rundunar soji daban-daban, hakan ya saka duk kokarin shugaba Buhari na kawo karshen aiyukan ta'addanci ya ki yin tasiri

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel