Ba mu ba zabe a jihar Legas muddin akan ci gaba da haramtawa Dalibai sanya Hijabi - MSSN

Ba mu ba zabe a jihar Legas muddin akan ci gaba da haramtawa Dalibai sanya Hijabi - MSSN

Kungiyar Musulmai ta daliban Najeriya watau Muslim Student Society of Nigeria, MSSN, ta gindaya wani babban sharadi na ko a yi ko a fasa ga dukkanin 'yan takarar kujerar gwamna na jihar Legas yayin babban zabe na shekarar badi.

Kungiyar MSSN reshen jihar Legas, ta gindaya sharadin ta na cewa ba bu wani dan takarar kujerar gwamnan jihar da za ta marawa baya a zaben 2019 face mai kudiri na halastawa Dalibai Mata sanya Hijabi a makaratun su na Sakandire.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan sharadi shine mafita na kare martabatar Mata da kuma addinin su na Islama da hakan zai tabbatar da tsare mutuncin su gami da kariya ta afkawa hannu miyagu masu kwazaba ta sha'awa.

Ba mu ba zabe a jihar Legas muddin akan ci gaba da haramtawa Dalibai sanya Hijabi - MSSN
Ba mu ba zabe a jihar Legas muddin akan ci gaba da haramtawa Dalibai sanya Hijabi - MSSN
Asali: Depositphotos

Shugaban kungiyar reshen jihar Legas, Saheed Ashafa, shine ya yi furucin hakan yayin gudanar da wata Lacca ta wayar da kai akan inganta jin dadin rayuwar al'umma da aka gudanar cikin birnin Legas a jiya Alhamis.

Ya ke cewa haramtawa Dalibai Mata sanya Hijabi musamman na makarantun Sakandire yana daya daga cikin mafi girman fasadi a ban kasa da ke nuni da cin zarafi gami da keta haddi da kuma haramta masu 'yancin su.

KARANTA KUMA: 2019: Dalilin da ya sanya mu ke da tabbacin nasarar Buhari - Oshiomhole

Mista Ashafa ya ci gaba da cewa, a duk sa'ilin da aka haramtawa Musulmai wani 'yancin su to kuwa ba bu kungiyar za ta fito kwanta da kwarkwata domin kare martabar su cikin lumana ba tare da tarzoma ba.

Kazalika jagoran kungiyar ya gargadi shugabannin makarantu masu hukunta Dalibai da suka sanya Hijabi duk da jan kunne da gwamnatin jihar ta yi na haramcin hakan. Ya kara da cewa hakan na barazana ga zaman lafiya a fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel