Duk da kashe-kashen da ake yi Gwamna Yari bai dawo Zamfara ba

Duk da kashe-kashen da ake yi Gwamna Yari bai dawo Zamfara ba

Labari ya kai gare mu daga Jaridar Daily Trust cewa duk da irin rikicin da ake yi a Jihar Zamfara cikin ‘yan kwanakin nan, gwamnan Jihar Alhaji Abdulaziz Yari yayi wata tafiya kuma har yanzu bai dawo ba.

Duk da kashe-kashen da ake yi Gwamna Yari bai dawo Zamfara ba
Gwamna Yari ba ya Zamfara yayin da ake ta kashe mutanen sa
Asali: Facebook

An dauki kwana da kwanaki yanzu haka Gwamna Abdul’aziz Yari ba ya gari yayin da aka kashe fiye da 40 a Jihar sa. An yi kusan makonni 2 kenan ana kai hare-hare a Garuruwan Zamfara irin su Birnin Magaji, Tsafe da sauran su.

Wannan kashe-kashen da ake yi dai ya jawo mutanen cikin Garin Tsafe sun fito sun yi zanga-zanga a Ranar Litinin dinnan. Wannan zanga-zanga da aka gudanar dai bai tunzura Gwamna Yari na Jihar ya dawo daga tafiyar da yayi ba.

KU KARANTA: Sarkin Tsafe ya bada umarni cafko wadanda suka yi zanga-zanga a Zamfara

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust, Abdulaziz Yari bai mika ragamar mulki a hannun Ibrahim Wakala, wanda shi ne mataimakin sa ba. Sai dai Yari ya zabi ya bar wa kakakin majalisar dokokin ragamar mulkin Jihar.

Yanzu dai Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji, wanda shi ne shugaban majalisar jihar, shi ne gwamnan rikon kwarya duk da cewa mataimakin gwamna Ibrahim Wakkala Mohammed yana nan. Wakala yana cikin masu harin kujeran Yari a 2019.

A wani bangare kuma, shugaban hafsun sojojin sama, Air Marshall Abubakar Siddique Mohammed ya sha alwashin maganin tsagerun da ke kashe jama’a a jihar Zamfara inda yace rundunar Operation Diran Mikiya za ta soma aiki gadan-gadan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel