Buhari ya gaza cika alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya - Atiku

Buhari ya gaza cika alkawuran da ya yiwa 'yan Najeriya - Atiku

- Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a ce shugaba Buhari bai aikata abubuwan da 'yan Najeriya suka zabe shi ya yi ba

- Atiku ya ce Buhari ya gaza wajen samar da shugabanci na gari, samar da tsaro, farfado da tattalin arziki da samar da ayyuka

- Atiku ya yi kira da magoya bayansa da sauran al'ummar Najeriya su zabe shi a 2019 domin shine zai iya kai Najeriya ga tudun na tsira

Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka - Atiku
Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka - Atiku
Asali: Facebook

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya gaza gaza alkawurran da ya yiwa 'yan Najeriya gabanin hawarsa kan mulki.

Atiku ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a Gombe yayin da ya ke jawabi ga magoya bayansa da 'yan jam'iyyar PDP a wurin bikin kaddamar da yakin neman zabensa ya yankin Arewa maso gabas kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu

Ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya gaza samar da ingantaccen shugabanci, samar da tsaro, farfado da tattalin arziki da samar da ayyuka ga dubban 'yan Najeriya da ke yawo a tituna.

Atiku ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a kasar nan musamman Boko Haram, garkuwa da mutane da kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi.

Ya yi kira ga masu kada kuri'a daga jihar Gombe da sauran jihohi biyar da ke mazabar su fito kwansu da kwarkwata su jefa masa kuri'a a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019 domin ya zama shugaban kasa ya kaddamar da shirye-shiryen da zai inganta rayuwar al'umma.

A jawabinsa, Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ce zaben 2019 za a gwabza ne tsakanin APC da miliyoyin 'yan Najeriya da ke rayuwa cikin mummunar talauci ta yadda basu iya cin abinci sau uku a rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel