Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

A shekarar 2013, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima ya auro mata daga kasar Misra wadda a lokacin wasu kafafen watsa labarai suka ce wai shekarun ta 13 da haihuwa.

Sai dai a hirar da Yerima ya yi da Daily Trust, ya ce matar da ya auro ta dara shekaru 13 amma bai bayyana ainihin shekarunta ba da cewa keta sirrin ta ne ya rika bayyana shekarunta.

A yayin da ya ke gwamna a jihar ta Zamfara, Yerima ya kawo tsarin Shari'ar addinin musulunci a gwamnati wadda daga baya wasu jihohi 11 a arewacin Najeriya suka yi koyi da shi.

A cikin 'yan kwanakin nan mutane sun gano wani hoton Yerima tare da wata mace mai siffar larabawa da kuma diya fara itama mai sifar larabawa a shafin Instagram kamar yadda shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Wasu shu'uman mata 2 da ke garkuwa da mutane a Kaduna sun shiga hannu

Shin ko wannan itace matarsa kuma yarinyar da ya ke rike da ita 'yar sa ne?

Masu bibiyar kafafen sada zumunta sunyi ta bayyana ra'ayoyinsu a kan mata da yarinyar da ke cikin hoton da Yerima inda wasu suka ce tabbas wannan matarsa ne duba da irin yadda suka kusanci juna a hoton.

Sai dai wasu kuma sun ce ba dole bane ta kasance matarsa saboda ana iya a halin yanzu akwai wasu 'yan siyasar da suke aikata wasu abubuwan da ba dole bane ya yi dai-dai da irin hudubar da suke yiwa al'umma.

Shin ko menene ra'ayin ku a kan hoton?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel