Ba girman Obasanjo bane yake sukar Buhari - Dattijon Sanata, Abdullahi Adamu

Ba girman Obasanjo bane yake sukar Buhari - Dattijon Sanata, Abdullahi Adamu

Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltan Nasarawa ta yamma a ya bayyana damuwarsa kan yadda tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ke sukar shugaba Muhammdu Buhari.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, Mr Adamu ya ce irin sukar da ya ke yiwa Buhari na zubda masa girma da kima.

Sanatan yana tsokaci ne a kan wani rahoto inda aka ce tsohon shugaban kasar ya ce shifa yana da dan takarar shugabancin kasa da ya ke goyon baya a zaben shekarar 2019 a maimakon ya rungumar kowa a matsayin na sa.

Ba girman Obasanjo bane yake sukar Buhari - Dattijon Sanata, Abdullahi Adamu
Ba girman Obasanjo bane yake sukar Buhari - Dattijon Sanata, Abdullahi Adamu
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Laifi ne saduwa a cikin mota - Hukumar 'yan sanda ta karyata jami'inta

Ya ce: "Duk da cewa yana da damar ya soki Buhari ko ya kira ga mutane kada su zabe shi, ya dace ya rika mutunta shi.

"Menene Obasanjo ya aikata yayin da ya rike mulki daga Fabrairun 1976 zuwa Oktoban 1979 da kuma Mayun 1999 zuwa Mayun 2007.

"Ai da batun tazarce karo na uku bai taso ba idan da ya tabuka abin arziki a lokacin da ya ke mulki kuma 'yan Najeriya shaidu ne."

A cewar Sanatan, a zamanin mulkin Obasanjo ne aka sayar da kadarorin Najeriya ba tare da wani amfani da aka samu daga hakan ba.

"Babu wani dan Najeriya nagari da ya san halin Obasanjo a baya da zai yi mamakin irin sukar da ya ke yiwa Buhari.

"Yana wuce gona da iri a maganganunsa kuma ina ganin ya dace masu fada a ji na kasar su ja masa kunne," inji dan majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel