Ba wan, ba kanin: Jam'iyyar AA taki amincewa da surukin Rochas

Ba wan, ba kanin: Jam'iyyar AA taki amincewa da surukin Rochas

- Surukin gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya sake fuskantar cikas a takararsa a gwamna

- Nwosu ya gaza samun tikitin takarar gwamna a jam'iyyar AA bayan ya fice daga APC saboda rashin samun tikitin

- Ciyaman din AA, Tunde Anifowose-Kelani ya ce Nwosu ba dan jam'iyyar AA bane kuma ba shine dan takarar gwamnan jam'iyyar ba

Shugaban jam'iyyar Action Alliance Party (AA) na kasa, Tunde Tunde Anifowose-Kelani ya ce Nwosu ba dan jam'iyyar AA bane ballantana jam'iyyar ta bashi tikitin takara a jihar Imo.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Tunde Anifowose-Kelani ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya bawa manema labarai a ranar Alhamsi 6 ga watan Disamba a Abuja.

Biyu babu: Surukin Okorocha ya rasa tikin takarar gwamna bayan a jam'iyyar AA bayan ya fice daga APC

Biyu babu: Surukin Okorocha ya rasa tikin takarar gwamna bayan a jam'iyyar AA bayan ya fice daga APC
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa ciyaman din jam'iyyar ya ce har yanzu Nwosu bai yi rajista a jam'iyyar AA ba saboda hakan babu yadda za ayi ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar a babban zabe mai zuwa.

A cewarsa, "A halin yanzu Uche Nwosu ba dan jam'iyyar mu bane saboda haka ba zai shigo ta bayan gida ya zama dan takarar gwamna a jam'iyyar a jihar Imo ba.

Shugaban jam'iyyar na AA ya ce jam'iyyar tana da dokoki da tsare-tsare da mutane za su bi idan suna son shiga jam'iyyar kuma ya zama dole duk mai son shiga jam'iyyar ya bi wadannan dokokin.

Kelani ya shawarci Uche Nwosu cewa idan yana son zama dan jam'iyyar Action Alliance AA, sai ya garzayo domin aikata abinda ya dace.

Uche Nwosu da wasu fusatattun mambobin jam'iyyar na APC a jihar Imo sun fice daga jam'iyyar ne saboda rikici-rikicen da ya dabai-baye jam'iyyar a yayin zabukkan cikin gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel