IG ya tura rundunar 'yan sanda 2000 domin yakar Boko Haram, hotuna

IG ya tura rundunar 'yan sanda 2000 domin yakar Boko Haram, hotuna

Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya tura karin wata runduna mai dauke da jami'an 'yan sanda 2000 zuwa jihar Borno domin yin aikin soji na yaki da 'yan ta'addar Boko Haram.

Rundunar ta kunshi jami'an 'yan sanda na musamman da su ka hada da ma su sintiri (PMF), ma su yaki da aiyukan ta'addanci (CTU), da kuma karnuka na musamman da aka bawa horo. An tura jami'an ne cikin kwanaki 2 da su ka wuce.

A sanarwar da rundunar 'yan sanda ta fitar, ta bayyana cewar IG ya tura karin jami'an 'yan sandan ne bisa dogaro da dokar aikin dan sanda na yin aiki soji a cikin gida domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al'umma.

IG ya tura rundunar 'yan sanda 2000 domin yakar Boko Haram, hotuna

IG ya tura rundunar 'yan sanda 2000 domin yakar Boko Haram
Source: Twitter

Source: Depositphotos

Tura karin rundunar 'yan sandan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun soji su ka yiwa kungiyar Boko Haram kamshin mutuwa ta fuskar rage yawaitar hare-haren da su ke kaiwa a jihar Borno da kewaye.

DUBA WANNAN: Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya

Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda, ya ce akwai jiragen yaki na hukumar 'yan sanda da aka tura zuwa jihar Borno domin bayar da taimako ta sama a yakin da jami'an da ke kasa zasu ke yi na kakkabe ragowar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

IG ya tura rundunar 'yan sanda 2000 domin yakar Boko Haram, hotuna

IG ya tura rundunar 'yan sanda 2000 domin yakar Boko Haram
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel