Kan zaman lafiya: Buhari ya yiwa 'yan Nigeria wa'azi, ya kafa hujjoji daga ayoyin Injila

Kan zaman lafiya: Buhari ya yiwa 'yan Nigeria wa'azi, ya kafa hujjoji daga ayoyin Injila

- Shugaban kasa Buhari ya shawarci 'yan siyasa da su kauracewa gurbata zabe ta hanyar kawo rabuwar kawunan a tsakanin Kirista da Musulmi

- Buhari ya bayyana kansa a matsayin Musulmi kuma wanda ya fito daga tsatson Annabi Ibrahim, tare da cewa Nigeria ce mai dauke da Kirista mafi yawa a kasashen Afrika.

- Ya ce ya samu matsin lamba daga masu kallonsa a matsayin wanda ke son Musuluntar da Nigeria, yayinda kuma Boko Haram ke zarginsa da juyawa Musulunci baya

A ci gaba da fuskantar zaben 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci 'yan siyasa da su kauracewa gurbata zaben ta hanyar kawo rabuwar kawunan a tsakanin manyan addinai biyu da ke a kasa, Kirista da Musulmi.

Shugaban kasa Buhari a cikin wata jaridar ra'ayi wacce ake wallafa a wata majami'a da ke UK ya bayyana kansa a matsayin Musulmi kuma wanda ya fito daga tsatson Annabi Ibrahim, ya bayyana cewa Nigeria ce mai dauke da Kirista mafi yawa a kasashen Afrika.

Ya ce ya kasance cikin matsin lamba daga mutanen da ke kallonsa a matsayin wanda yake son Musuluntar da Nigeria, yayinda a hannu daya kuma Boko Haram ke zarginsa da juyawa Musulunci baya, yana mai cewa hatta shi kansa mataimakinsa, Yemi Osinbajo wanda takiyyin Kirista ne an zargeshi da sayar da addininsa kawai don yana goyon bayansa (Buhari).

KARANTA WANNAN: Yahoo Yahoo: An gurfanar da 'yan Nigeria 2 a Ghana da laifin damfara ta yanar gizo

Kan zaman lafiya: Buhari ya yiwa 'yan Nigeria wa'azi, ya kafa hujjoji daga ayoyin Injila

Kan zaman lafiya: Buhari ya yiwa 'yan Nigeria wa'azi, ya kafa hujjoji daga ayoyin Injila
Source: Depositphotos

Shugaban kasar ya ce, "A shekarar 1844, Revd Samuel Ajayi Crowther ya dawo kasarsa ta Yoruba (wacce a yanzu take shiyyar Nigeria). A shekaru 20 kafin lokacin, an kamashi an sayar da shi ga Turawan yamma a matsayin bawa. Ya samu kubuta ta silar wasu jami'an sojin ruwa inda ya samu tarba daga kungiyar majami'u masu yayata addinin Kirista.

"Kamar dai yadda milliyoyi daga al'ummar Kirista a Nigeria suke tunani a yau, nima ina da yakinin cewa ta hanyar zaman lafiya, kaunar juna da kuma sasanci; a tsari na zaman iyali, a tsari "na auratayya, a kyakkyawan yakini, Nigeria zata samu daukaka fiye da tunanin kowa.

"Kamar dai Bishop Crowther, nima na fito ne daga tsatson Abraham; sai dai ba kamar shi ba, ni Musulmi ne. Ina da yakinin cewa manyan addinanmu guda biyu ba wai zasu karu ta hanyar zama lafiya ba, a'a, hatta ta hanyar jin kan juna.

"Sai dai ya zama wajibi Musulmai da Kirista su kasance masu kare dayansu. Domin kuwa an fadi haka a cikin littafin Amos, sura ta 3 aya ta 3, cewa: "Mutane biyu ba zasuyi tafiya tare ba, har sai idan sun yarda ne su hadu?"

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nuni da cewa, ta hanyar fadar Allah S.W.A "Babu tilaci a cikin addini" (Qur’an 2.256) kamar yadda take cewa: "Karku hana shi: wanda ya nuna baya tare damu wani abu mallakinsa" (Injila: Luke 9.50), Don haka ya ce akawai bukatar addinan biyu su kasance masu kaunar zaman lafiya don ci gaban kasar baki daya yana mai kafa hujja da: "Shin kuna da idanuwa amma ba zaku iya gani ba, kuma kuna da kunnuwa amma ba zaku iya ji ba?" (Injila: Mark 8.18)

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel