Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 5 a jihar Enugu

Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 5 a jihar Enugu

Mun samu cewa kimanin rayukan Mutane biyar sun salwanta a sanadiyar wani mummunan hatsarin mota da auku da sanyin safiyar jiya ta Alhamis a birnin Enugu kamar yadda hukumar tsaro ta 'yan sanda reshen jihar ta bayyana.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, babban jami'in hulda da jama'a na hukumar, SP Ebere Amaraizu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Enugu a yau Juma'a.

SP Amaraizu ya bayyana cewa, wannan tsautsayi da ya auku tsakanin Motoci biyu a babbar hanyar garin Abakaliki daura da yankin Emene, kwatsam ba tare da aune ba ya yi sanadiyar katse hanzarin Mutane biyar akan hanyarsu ta sufuri.

Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 5 a jihar Enugu
Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 5 a jihar Enugu
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi gaggawar garzayawa da wannan Mutane biyar zuwa asibitin kurkusa na cibiyar lafiya ta da ke yankin Emene, inda Likitoci suka tabbatar da Mutuwarsu nan take.

KARANTA KUMA: Majalisar Tarayya ta fiye tsanani da rashin godiya - NNPC

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya sanya aka killace gawarwakin Mutane biyar da rayukan su suka salwanta a dakin ajiyar gawa na cibiyar lafiyar ta Emene kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rayukan Mutane biyar sun salwanta tare da jikkatar Mutane 2 a sanadiyar wani mummunan hatsari da ya auku cikin jihar Ogun a ranar Talatar da gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel