Gwamnan Cross River, Ayade ya caccaki PDP a bainar jama'a kan zaben fitar da gwani

Gwamnan Cross River, Ayade ya caccaki PDP a bainar jama'a kan zaben fitar da gwani

- Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya caccaki jam'iyyar PDP sakamakon irin aika-aikatar da ya ke kallon jam'iyar ta tafka a zaben fitar da gwani a jihar

- Duk da cewa babu inda gwamnan ya ambaci sunan jam'iyyar har ya kammala jawabi wajen taron, sai dai, kowa da ke wajen ya san jam'iyyar da gwamman ke la'anta

- Ya la'anci jam'iyyar ne a karo na farko a wani taron kaddamar da wani bankin 'yan kasuwa a Calabar

Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya caccaki jam'iyyar PDP tare da kiranta da munanan sunaye sakamakon irin aika-aikatar da ya ke kallon jam'iyar ta tafka a zaben fitar da gwani na mazabar jihar ta tsakiya.

Duk da cewa babu inda gwamnan ya ambaci sunan jam'iyyar har ya kammala jawabi wajen taron, sai dai, kowa da ke wajen ya san jam'iyyar da gwamman ke la'anta.

Da ya ke jawabi a karo na farko a wani taron kaddamar da wani bankin 'yan kasuwa a Calabar, Ayade, wanda ya kira Agara ya zo ya tsaya kusa da shi a wajen gabatar da jawabin, ya ce, "Zan so in kira dan uwana, Chris Agara, da ya taimaka ya taso yazo ya tsaya nan kusa da ni. Ya zo mu la'anci shegiyar uwa. Mu la'anci shedan da duk wasu makiyanmu. Mu la'anci dukkanin wadanda ke hada yan uwa fada. Ka sani, ina maraba da kai dan uwana."

KARANTA WANNAN: Har yanzu mambobin APC na tare da Buhari duk da suna fushi da Oshiomhole - Uche Uwosu

Gwamnan Cross River, Ayede ya caccaki PDP a bainar jama'a kan zaben fitar da gwani
Gwamnan Cross River, Ayede ya caccaki PDP a bainar jama'a kan zaben fitar da gwani
Asali: Facebook

Ayade ya ce Agara ne dan uwansa, wanda zai iya sadaukar da kwayar idonsa don kare martabarsa, wanda kuma ko a cikin tsanani, da dukkanin abokan gabar da ke kawo suka kullum, ya jajurce don kar a cutar da shi, wanda hakan ya zama tilas a gareshi ya cire siyasa don 'yan uwantaka.

"Kowa ya ga yadda Chris Agara ya kashe makudan kudade fiye da sauran 'yan takara a jihar, amma saboda rashin adalci irin na jam'iyyar, sai da mutum ya shirya ya zo wajen zabe, sannan ne za a cire sunansa daga jerin 'yan takara.

"Kun cire sunansa ne kawai saboda kunsan yana da karfi. Don haka akan dan uwana, ina shawartarka da ka jajurce da kuma bin dokokin ubangiji, don haka Allah ya tsara. Amma ga wadanda shedan ya yiwa fitsari suka dakatar da kai, suka yi fito na fito da Allah akan ka, to Allah ya tarwatsa su da wuta mai zafi.

"Shedan zai tashi, fatalwa ma zata tasi, amma idan Almasihu ya tashi, zai kakkabe su gaba daya kuma ya samar da zaman lafiya, ya dawo da martabar 'yan uwan taka. Zamu basu mamaki. Shi ne zai bamu sa'a a yakin zabenmu, ya sa mu gudu tare mu tsira tare wajen gina jihar Cross River," a cewar gwamnan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel