Daga karshe, Buhari ya yi magana kan bidiyoyin zargin cin hancin Ganduje
A yau Litinin, shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan zargin da ake yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda yace za'a dau mataki kan al'amarin.
Jaridar Daily Nigerian ta bada rahoton cewa Shugaba Buhari ya yi wannan magana ne yayinda wani dalibi dan asalin jihar Kano a kasar Faransa yabi irin ayyukan da gwamnan keyi kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya ta bi sahunsa.

Asali: Depositphotos
Kan ya gama magana, shugaba Buhari ya tambayi dalibin shin ya ga bidiyon da aka nuna gwamnan yana karban daloli?
Yace: "A bangare guda, shin baka ga bidiyoyin gwamnan inda yake cusa daloli cikin garensa ba?"
"Mun baiwa hukumomin tsaro bidiyoyin domin bincike. Kuma za mu dau mataki akan abin inda aka same shi da kashe a gindi."
Amma Wannan abu bai yiwa dan majalisan wakilan jihar Kano mai wakiltan Nasarawa, Nassir Ali-Ahmed da kuma hadimin shugaban kasa Sha'aban Sharada, wadanda suka bukaci yan jarida su taimaka su cure inda shugaba Buhari yayi wannan furuci.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng