An kashe ma su sayar da kayan gwari 2 a sabon rikicin Jos

An kashe ma su sayar da kayan gwari 2 a sabon rikicin Jos

- An kashe mutane 2 tare da raunata wasu uku a sabon rikicin da ya barke da yammacin jiya, Lahadi, a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato

- Rahotanni sun bayyana cewar an kashe mutanen biyu ne yayin da su ke dawowa daga gona

- An kai harin ne a yankin Nding Sestu mai makwabtaka da kasuwar 'yan dankali a karamar hukumar Jos ta kudu

Mutane biyu aka kashe tare da raunata wasu uku a sabon rikicin da ya barke da yammacin jiya, Lahadi, a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewar an kashe mutanen biyu ne yayin da su ke dawowa daga gona.

Kazalika an bayyana cewar wadanda su ka kawo harin sun tsere da wata motar daukan kaya da ke cike da kayan miya.

An kashe ma su sayar da kayan gwari 2 a sabon rikicin Jos
Gwmnan jihar Filato, Simon Lalong
Asali: UGC

Fodio Umar, wani mai sana'ar sayar da kayan miya da na gini a kasuwar karamar hukumar Jos ta kudu, ya bayyana cewar dukkan mutanen da aka kashe mazauna garin Barkin Ladi ne.

Umar ya kara da cewar an binne mutanen biyu safiyar yau, Litinin.

Duk da bai samu damar amsa kiran da aka yi masa ba, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, Tyopev Tarner, ya tabbatar wa da jaridar Premium Times batun kisan mutanen ta hanyar takaitaccen sakon waya.

DUBA WANNAN: Machina: Gari a arewa da macizai ke kaiwa Sarki gaisuwa

Kazalika, kwamandan rundunar soji ta Ofireshon safe haven, Adam Umar, ya tabbatar da batun kai harin.

"An kai harin ne a yankin Nding Sestu mai makwabtaka da kasuwar 'yan dankali.

"Jam'ian mu sun gaggauta zuwa wurin amma bayan isar sun samu mutane biyar da aka harba, amma daga baya an tabbatar da mutuwar biyu daga cikinsu bayan an kai su babban asibitin garin Barkin Ladi," a cewar Umar.

Umar ya kara da cewar dakarun soji na aiki, ba dare ba rana, domin ganin an kama wadanda su ka kai harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel