Abin tausayi: An gano gawar yara 2 da kare 1 a cikin firinji a Legas

Abin tausayi: An gano gawar yara 2 da kare 1 a cikin firinji a Legas

- Mazauna unguwar Ikorodu a jihar Legas sun shiga cikin juyayi bayan gano gawar wasu yara biyu da kare daya a cikin na'urar sanyaya ruwa

- Wani makwabcin gidan ya shaidawa NAN cewar yaran na tare da mahaifinsu a gida ranar da lamarin ya faru

- NAN ta rawaito cewar an garzaya da yaran asibiti amma sun sanar da iyayensu cewar yaran sun rigaya sun mutu

Mazauna unguwar Ikorodu a jihar Legas sun shiga cikin juyayi bayan gano gawar wasu yara biyu da kare daya a cikin na'urar sanyaya ruwa (firinji).

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar lamarun ya faru ne a gida mai lamba 2 da ke kan titin Christian Onoja da misalin karfe 4:30 na yamma.

Wani makwabcin gidan ya shaidawa NAN cewar yaran; Emmanuel Edeh (mai shekaru 7) da Darasimi Edeh (mai shekaru 4) na tare da mahaifinsu, Mista Michael Edeh, a ranar da lamarin ya faru.

Abin tausayi: An gano gawar yara 2 da kare 1 a cikin firinji a Legas
Firinji
Asali: Twitter

"A ranar Lahadi da rana, sai mahaifinsu ya fito yana tambayar inda yaransa su ke.

"Sai mu fara duba gidajen makwabta amma ba mu ga yaran ba," a cewar makwabcin.

Majiyar ta kara da cewa bayan an gaza gano inda yaran su ke ne sai aka kira mahaifiyar su, kuma ba a dade da dawowar ta ba ne ta gano gawar yaran a cikin firinjin gidansu.

DUBA WANNAN: Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70, hotuna

NAN ta rawaito cewar an garzaya da yaran asibiti amma sun sanar da iyayensu cewar yaran sun rigaya sun mutu.

Da kamfanin NAN ya tuntubi asibitin Briggston da aka kai yaran bayan gano gawar su, ya bayar da tabbacin cewar an kawo yaran ne babu rai.

Kazalika, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ya tabbatar wa da NAN cewar an sanar da kwamishinan 'yan sanda batun samun gawar yaran tare da karen gidansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel