Hadi Sirika ya bayyana dalilin yiwa jirgin Atiku binciken kurilla

Hadi Sirika ya bayyana dalilin yiwa jirgin Atiku binciken kurilla

Ministan kula da harkokin jirgin sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewar binciken da aka yiwa jirgin dan Atiku ba wani sabon abu ba ne a tsarin aikin jami'an tsaro da ke aiki a filayen tashi da saukar jiragen sama da ke fadin kasar nan.

A yau ne dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi korafin cewar an tozarta shi bayan ya sauka a Najeriya.

Atiku ya dawo Najeriya a yau, Lahadi, bayan shafe kwanaki da dama a kasar Dubai inda ya yi taro da magoya bayansa domin tsara yadda za su tunkari zaben shekarar 2019.

A wani jawabi da fadar shugaban kasa ta fitar mai dauke da sa hannun Sirika, an zargi Atiku da yunkurin neman suna ta hanyar yada farfaganda.

Hadi Sirika ya bayyana dalilin yiwa jirgin Atiku binciken kurilla
Atiku a filin jirgin sama
Asali: Facebook

"Muna son sanar da jama'a cewar dole ne duk jirgin da ya shigo Najeriya sai jami'an hukumar kwastam da na hukumar kula shige da fice ta kasa da ragowar jami'an tsaro sun yi bincike a jirgin.

"Dokar ba ta ware jirage na manyan mutane ko na haya (shata) ba.

DUBA WANNAN: Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

"Akwai bangaren tashi da saukar shugaban kasa, nan ne kadai jami'an tsaro ba sa duba jirgin da ya sauka a bangaren.

"Atiku dan takara ne, kuma bai kamata a matsayinsa na mai son shugabantar jama'a ya yi korafin an yi aiki da dokar kasa a kansa ba," a cewar Sirika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel