Rikicin Kaduna: Unguwanni 5 da zasu cigaba da zama a cikin gida na tsawon awanni 24

Rikicin Kaduna: Unguwanni 5 da zasu cigaba da zama a cikin gida na tsawon awanni 24

Gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da sassauta dokar ta bacin da ta sanya a garin Kaduna, na ba shiga ba fita, a ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba sakamakon rikicin addini daya barke a gari.

A sanarwar da gwamnatin jahar ta fitar a ranar Talata ta bakin Kaakakinta Samuel Aruwan, tace an sassauta dokar a garuruwan kasuwar magani da Kujama daga hana shiga da fita na awanni 24, zuwa fita da shiga daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Omoyele Sowore ya zabo mataimakinsa daga jahar Jigawa

Haka zalika LEGIT.com ta ruwaito sanarwar ta cigaba da fadin sassaucin dokar hana shiga da fitan ya shafi dukkanin unguwannin Kaduna, amma za ayi hada hada ne kadai daga karfe 1 na rana zuwa 5 na yamma.

Rikicin Kaduna: Unguwanni 5 da zasu cigaba da zama a cikin gida na tsawon awanni 24
Nasir
Asali: Facebook

Sai dai duk da wannan sassauci da gwamnatin tayi, akwai sauran yankunan garin Kaduna da gwamnati bata daga ma kafa ba, daga cikin unguwannin nan akwai Narayi, Kabala West, Kabala Doki, Mararraban Rido da Sabon tasha.

“Biyo bayan taron majalisar tsaro da gwamnan jahar Kaduna yayi da shuwagabannin hukumomin tsaro daya gudana a ranar Talata da misalin karfe 9 na safe, majalisar ta yanke shawarar sassauta dokar hana shiga da fita a Kasuwar magani da Kujama daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma.

“Sai dai majalisar ta lura akwai sauran barazana a unguwannin Kabala west, Kabala doki, Sabon tasha, Narayi da maraban rido, don haka dokar awa 24 na nan a wadannan yankuna, don haka duk wanda ya karya dokar zai fuskanci tsatstsauran hukunci.

“Amma majalisar ta lura akwai cigaba game da zaman lafiya a sauran unguwannin garin Kaduna, don haka an dage dokar fita zuwa daga karfe 1 na rana zuwa 5 na yamma, don baiwa kasuwanni damar budewa.” Inji shi.

Daga karshe majalisar ta bayyana rashin jin dadinta da yadda jama’a suka takura bisa wannan doka, amma an dauki matakin ne don tsaron rayukan jama’a da dukiyoyinsu, don haka gwamnati ba zata yi sakwa sakwa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel