Hanyoyin magance rikicin Kaduna

Hanyoyin magance rikicin Kaduna

Tun bayar barkewar rikici a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuma ta jihar Kaduna a ranar Juma'a da ta gabata, gwamnati ta saka dokar hana fita na sa'o'i 24 a garin na Kaduna.

Rahotannin da 'yan sanda suka bayar ya nuna cewa mutane 55 ne suka rasa rayyukansu sakamakon rikicin kuma daga baya 'yan sandar sun sanar da cewar sun kama mutane 22 da ake zargi da hannu cikin tayar da rikicin wadda za'a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.

Hanyoyin magance rikicin Kaduna
Hanyoyin magance rikicin Kaduna
Asali: Facebook

Wannan dai ba shine karo na farko da irin wannan rikicin ke afkuwa a jihar ba hakan yasa wani jarida kuma mai sharhi kan sha'anin rikicin Kaduna, Abdul-Azeez Ahmed Abdulkadir ya bayyana wasu matsaloli da ya ke ganin ya dace a warware su idan ana son kawo karshen rikice-rikice a jihar kamar yadda BBC ta ruwaito.

1. Rashin daukar mataki daga bangaren gwamnati

Masanin ya bayyana cewar rashin daukar mataki daga bangaren gwamnatoci da suka shude yana daya daga cikin dalilin da yasa har yanzu rikicen ke cigaba da afkuwa.

Yana ganin muddin ba a gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu cikin rikicin gaban kotu kana an yanke musu hukuncin da ya dace da su ba tabbas a nan gaba ma wasu za su sake tayar da fitinar.

DUBA WANNAN: Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

2. Karancin Alkalai

Masanin ya ce babu wadatattun alkalai a jihar Kaduna, hasali ma adadin alkalan jihar ba su kai rabin abin da ake bukata a jihar ba domin hukunta masu laifi wanda hakan ke sanya ayi ta jinkirta shari'a har illa masha Allah.

Ya kuma ce akwai batun rashin iya tattara shaidu da hukumomin tsaro a jihar ba su iya yi wadda hakan ke nufin alkalai ba za su iya yanke hukunci ba.

3. Siyasa

Wani mai nazari kan lamurran tsaro a Najeriya, Mallam Kabiru Adamu ya bayyana cewar 'yan siyasa ba su son daukar matakan da ya dace na hukunta masu laifi ne saboda gudun sabawa wasu kabilu ko addinai.

Ya ce suna fargabar rasa kuri'un kabilu ko mabiyan addinai idan an hukunta mabiyansu.

A jawabin da gwamna El-Rufa'i ya yi a jiya, ya ce ba za'a sassutawa duk wanda aka tabbatar da hannunsa cikin rikin ba har ma da wadanda aka kama a wani rikicin da ya faru a baya.

Ya ce da zarar gwamnati ta fara hukunta wadanda aka samu da laifin, hakan zai zama darasi ga al'umma kuma zai taimaka wajen kawo karshen rikicin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel