Zamu qawata Najeriya ta yadda matasan mu zasu dena sha'awar fita Turai - Buhari
- Shugaba Muhammadu Buhari ya koka kan yadda matasa ke jefa rayurwarsu cikin hadari domin zuwa kasashen Turai ba bisa ka'ida ba
- Shugaban Kasar ya dau alwashin kawo gyara a kasar ta yadda za ta kasance abin alfahari ga dukkan 'yan kasar
- Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a wajen liyar ban kwana da aka shirya wa jakadar jamhuriyar Namibia a Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa matasan Najeriya cewar gwamnatinsa za ta yiwa Najeriya gyarar da zai saka matasa su dena kwadayin zuwa kasashen waje da Teku ko Sahara domin zuwa ayyukan kwadago.
Shugaba Buhari ya bayyana cewar irin wannan tafiye-tafiyen na da hatsari sosai kuma yana zubda mutuncin Najeriya a idanun kasashen duniya.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama wasu matasa maza da mata 14 suna tika rawa zigidir a jihar Kebbi
Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata a fadar gwamnati yayin liyafar bankawana da aka shiryawa Babban Kwamisihinan Jamhuriyar Namibia Mr. Peingeondjabi Shipoh.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen yada labarai, Femi Adesina, Buhari Najeriya da Namibia za su amfani juna ta fannin kasuwanci da Noma.
Shugaba Buhari ya koka kan yadda matasa ke jefa kansu cikin hatsari yayin kokarin haurawa kasashen Turai ba bisa ka'ida ba duk da irin albarkatun da ke nahiyar inda ya dau alwashin tabbatar da ganin ya kawo gyara a Najeriya ta yadda matasan ba su suyi kwadayin fita ba.
Asali: Legit.ng