Cacar baki tare da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin Dino Melaye da Akpabio

Cacar baki tare da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin Dino Melaye da Akpabio

Yayan majalisar dattawa wadanda aka fi sani da suna Sanatoci sun shiga nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki akan wata karamar matsala da bata taka kara ta karya ba, matsalar itace tsarin da sanatocin zasu zauna a majalisar, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wadanda suka rura wannan matsala sune Sanatan jahar Kogi dan PDP , Dino Melaye da Sanatan jahar Akwai Ibom dan APC, kuma tsohon gwamnan jahar, Godswill Akpabio.

KU KARANTA: Shari’ar Shema: Babbar kotun tarayya ta sanar da ranar yanke hukunci akan wata sarkakiya

Wani Sanata dan jam’iyyar PDP, kuma ya fito daga jahar Akwai Ibom, Sanata Bassey Akpan ne ya fara tayar da wata magana a karkashin kudurin ra’ayin kashin kai, inda yace ya samu labari cewar jam’iyyar APC na shirin janyo rikici a jahar Akawa Ibom a yayin zaben 2019, wanda zai kai ga soke zaben jahar.

Cacar baki tare da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin Dino Melaye da Akpabio
Majalisa
Asali: UGC

Jin haka yasa Sanata Akpabio, wanda duk da cewa Sanata Bassey bai kira sunansa ba, amma hannun sanda yayi masa, ya daga hannu yana neman shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki ya bashi damar mayar da martani, amma Saraki ya hana shi.

Uzurin da Sanata Bukola Saraki ya bayar na hana Sanata Akpabio mayar da martani shine kan cewa kujerar da Sanata Akpabio ke zaune a kai bata da na’urar yin magana, don haka ko yayi magana babu wanda zai ji shi da kyau.

Amma da Sanatan ya dage akan lallai sai ya mayar da martani, sai Saraki ya bashi shawarar ya canza kujerar zama, ya koma kujerar dake dauke da na’urar yin magana amsa kuwwa, ana cikin haka ne sai Dino ya tashi daga kujerarsa saboda a Akpabio na ta daga murya akansa.

Bugu da kari sai shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmed Lawan ya kara tada wata magana na cewa a yanzu babu wata tsarin zama a majalisar sakamakon wasu sanatoci sun sauya sheka daga jam’iyyar da aka zabesu, anan ma wasu Sanatocin APC sun bayyana ma Saraki cewa yana nuna musu wariya.

Fadin wannan maganar ce ta janyo aka dinga musayar yawu, caca baki, cece kuce tare da nuna ma juna yatsa tsakanin Sanataocin APC da na PDP, hatsaniyar da ta kwashe kimanin mintuna talatin ana yinta.

Daga bisani Akpabio ya samu damar magana, amma Dino yana ta katse shi, daga nan sai ya tsaya ya nemi aba shi hakuri saboda an bashi kujerar da bata da na’aurar yin magana, kuma akawun majalisa ne ya bashi, amma akawun ya musanta batun Sanata, inda yace Sanatan ne ya matsa lallai sai na bar masa kujerar.

Daga karshe Sanata Akpabio ya nemi gafarar majalisa, sa’annan yace ya fasa magana har sai ranar da aka gyara batun tsarin zaman Sanatoci a zauren majalisar dattawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel