'Yan sanda sun gayyaci dan takarar gwamnan Kano na PDP kan kisan tsoho dan shekara 70
- 'Yan sanda sun gayyaci dan takarar gwamnan Kano na PDP kan kisan tsoho dan shekara 70
- Sun ce ya kai kan sa wajen kwamishinan su
- Magoya bayan sa ake zargi da kisan tsohon
Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano sun aike da takardar sammaci suna gayyatar dan takarar kujerar gwamnan Kano, Alhaji Sagir Abdullahi Takai bisa mutuwar wani tsoho mai shekaru 70 a duniya lokacin da ya ke gudanar da gangami.

Asali: UGC
KU KARANTA: Hotunan jaruma Maryam Yahaya da suka kayatar
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan SP Magaji Majiya ya bayyana cewa suna sa ran dan takarar zai mika kansa ga kwamishin 'yan sandan jihar don girmama gayyatar da suka yi masa da kuma ansa wasu 'yan tambayoyi a ranar Litinin mai zuwa.
Legit.ng dai ta samu cewa ana zargin wasu daga cikin masoyan dan takarar ne suka kashe tsohon sakamakon dukan da suka yi masa da muggan makamai ranar Asabar din da ta gabata lokacin wani gangami da suka yi a kan hanyar zuwa Hadejia.
A wani labarin kuma, Wani matashi dan shekara 23 mai suna Adamu Mohammed da ya gawurta a wajen luwadi da kananan yara a karamar hukumar Chanchaga, jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya ya bayyana dalilin da yasa ya zabi yin luwadi a rayuwar sa.
Adamu wanda yanzu haka yake a hannun 'yan sandan jihar, ya shaidawa 'yan jarida cewa ya zabi zama dan luwadi ne sakamakon kasantuwar maza basu yin ciki kamar mata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng