Rikicin Jos: Majalisa ta nemi Jami’an tsaro su gudanar da bincike a Najeriya

Rikicin Jos: Majalisa ta nemi Jami’an tsaro su gudanar da bincike a Najeriya

Mun ji cewa Honarabul Edward Gyang Pwajok wani ‘Dan Majalisan APC daga Jihar Filato ya nemi a hana Sojojin Najeriya binciken da su ke yi game da wani babban Sojan Najeriya da aka kashe a Garin Jos.

Rikicin Jos: Majalisa ta nemi Jami’an tsaro su gudanar da bincike a Najeriya
Shugaban Majalisa Yakubu Dogara ya nemi Jami'an tsaro su duba rikicin Jos
Asali: Twitter

Honarabul Edward Pwajok wanda ke wakiltar Gabas da Kudancin Jos a Majalisa ya nemi Sojojin Najeriya su zare hannun su daga binciken kisan da aka yi a Filato inda ya nemi a bar wa Jami’an ‘Yan Sanda da kuma DSS wannan aiki.

‘Dan Majalisar da ya kawo wannan batu a zaman jiyan, babban Lauya ne wanda ya kai matakin SAN, ya bayyana cewa binciken zai fi kyau idan aka bar Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda su ka gudanar da shi domin su ke da hurumin hakan a dokar kasa.

KU KARANTA: 2019: Mutanen Kano sun rasa makama a Jam’iyyar PDP

Aliyu Madakin-Gini wanda yake wakiltar Yankin Dala ta Kano a Majalisar Wakilan Tarayyar bai amince da wannan ba inda yayi tir da bukatar abokin aikin na sa. Madakin-Gini yace bai kamata ace Sojoji su daina wannan bincike mai amfani ba.

Hon. Madakin Gini ya koka da yadda ake kashe mutane dare da rana a kasar nan saboda banbancin kabila da addini inda yayi kira a gudanar da bincike domin jin abin da yayi sanadiyyar mutuwar Janar A. Alkali da wani Kyaftin Mwankon Gyang.

Edward Gyang Pwajok yana ganin idan aka damka wannan aikin a hannun ‘Yan Sanda, za a fi kare hakkin Bil Adama a yayin gudanar da binciken inda yayi tir da duk abin da ya faru a Jihar ta Filato.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel