Wata Musulma ta samu nasara a kotu kan tuhumarta da kin musabaha da wani namiji a yayin jarabawar daukar aiki

Wata Musulma ta samu nasara a kotu kan tuhumarta da kin musabaha da wani namiji a yayin jarabawar daukar aiki

Rahotanni sun kawo cewa wata matashiyar Musulma ‘yar kasar Sweden ta samu nasara a kotu kan wata tuhuma da ake yi mata.

Ana dai tuhumarta ne da kin mika hannu ta yi musabaha da wani namiji a lokacin da aka yi mata jarabawar daukar aiki.

Farah Alhajeh, mai shekara 24, tana neman aikin fassara ne a wani kamfani, lokacin da ta ki amincewa ta gaisa da mutumin da ke jagorantar jarabawar daukarta aiki saboda tsoron kada ta saba wa addininta.

Wata Musulma ta samu nasara a kotu kan tuhumarta da kin musabaha da wani namiji a yayin jarabawar daukar aiki
Wata Musulma ta samu nasara a kotu kan tuhumarta da kin musabaha da wani namiji a yayin jarabawar daukar aiki

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An nada Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakin hukumar DSS

A ranar Alhamis ne wata kotun ma’aikata ta kasar ta yanke hukuncin cewa an nuna wa Farah bambanci kuma ta umarci kamfanin da ya biyata diyyar dala 4,350 (kimanin naira miliyan daya da rabi).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel