Ana samun raguwar tsadar farashin kayan masarufi a Najeriya - NBS

Ana samun raguwar tsadar farashin kayan masarufi a Najeriya - NBS

- Tsadan kayan masarufi na cigaba da raguwa a shekarar nan

- Alkaluma sun nuna cewa hauhuwar farashi yana ta raguwa

Ana samun raguwar tsadar farashin kayan masarufi a Najeriya - NBS

Kaya na rage tsada a Najeriya a yanzu inji Hukumar NBS

Mun samu labari cewa a halin yanzu ana cigaba da samun saukin farashin kayan abinci a Najeriya. A Gwamnatin Buhari dai abubuwan sun tsawwala ta bangaren kudin kayan masarufi a farkon kafuwar wannan Gwamnati.

Alkaluman da Hukumar NBS ta saki kwanan nan sun nuna cewa kayan masarufi na rage kara kudi ne a Najeriya. An samu raguwar hauhawar tsadar kaya zuwa kashi 11.14%, a watan jiya dai alkaluman sun tsaya ne a kan kashi 11.23%.

KU KARANTA: An kashe wata gobara da kyar a cikin Garin Legas

Watanni kusan 17 kenan a jere kayan masarufi su na cigaba da rage tsada a Najeriya. Tun Junairun 2017, ba a taba jin cewa kaya sun kara tsada a Kasar ba. Hukumar da ke tara alkaluma na kasar ta fito da rahoton nan ne kwanan nan.

Idan ma dai aka kamanta saukin tsadar kaya daga watan jiya da na wannan wata, za a ga cewa ba a samu wani raguwar farashi kamar yadda aka samu a baya ba. Sai dai duk da haka, ana samun sauki a halin yanzu ba kamar 2016 ba.

Kwanakin baya kun ji labari cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘Yan Najeriya albishir da cewa abubuwa na cigaba da kara kyau a Gwamnatin sa. Buhari yace abubuwa sun mike ta fuskar tattalin arzikin kasar a halim yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel