Hanyoyin Sama wa Matasa aikin yi da habaka arzikinsu - CBN da LYNX

Hanyoyin Sama wa Matasa aikin yi da habaka arzikinsu - CBN da LYNX

- An gano hanyoyin ilimantar da matasa

- Sana'o'in dogaro da kai ma suna taka rawar gani gurin taimakon matasa

- Ilimin sanin kudade na da amfani

Hanyoyin Sama wa Matasa aikin yi da habaka arzikinsu - CBN da LYNX
Hanyoyin Sama wa Matasa aikin yi da habaka arzikinsu - CBN da LYNX

Babban bankin Najeriya tare da Linking the Youth of Nigeria through Exchange(LYNX) sun gano hanyoyin ilimantar da matasa domin zama masana harkar kudi don dogaro da kai a shekaru kadan.

Wakilin babban bankin Najeriya yayi magana a wani taro a Abuja.

Abubakar Albasu ya jaddada akan wadansu abubuwan da ya kamata a kara akan ilimin sanin kudi. Albasu yace ilimin na da tsananin amfani.

Ya kara da cewa babban bankin Najeriya tana maraba da duk wani hadaka da zata taimaka gurin koyar da ilimin sanin kudi.

DUBA WANNAN: Hanyoyin kiwon lafiya: Inji bankin Duniya

A bangaren ta kuwa, National Programme Officer, LYNX, Ganiyu Ibikunle ta bayyana cewa kungiyar su ta horar da sama da matasa 30,000 a Najeriya daga 2004 zuwa yanzu.

Ibikunle ta bukaci hadaka daga cibiyoyin gwamnati da kungiyoyi don tabbatar da cewa yara da matasa sun samu ilimin kudi domin su iya amfani da salon kirkira.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng