Babbar magana: Karuwan Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki

Babbar magana: Karuwan Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki

Karuwai a Najeriya daga jihar Anambra sun yi barazanar shiga yajin aikin da zai haramtawa dukkan abokan sana'ar su kwanciya da 'yan sandan Najeriya bisa zargin muzguna masu da suke yi a wuraren sana'ar su.

Kamar yadda muka samu, daya daga cikin karuwan da ta tattauna da wakilin majiyar mu ta bayyana cewa hakika yanzu tura ce ta kai su bango don kuwa sun gaji da irin cin kashin 'yan sandan kasar ke yi masu musamman ma a garuruwan Umunze da Orumba.

Babbar magana: Karuwan Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki
Babbar magana: Karuwan Najeriya sun yi barazanar shiga yajin aiki
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kotun kasa-da-kasa ta karyata fadar shugaban kasa

Legit.ng ta samu cewa karuwan dai sun bayyana cewa za su bar kwanciya da 'yan sandan da ta ce kusan sune rabin kwastomomin su idan dai har basu gyara ba daga ranar Litinin mai zuwa.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyar mu ta BBC Hausa na nuni ne da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga dadi ne sun harbe wasu Hausawa masu sana'ar canjin kudaden kasar waje a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya.

Kamar dai yadda muka samu wadanda aka kashen din sun hada da Ahmad A. Tukur da Yusuf Zaki da Muhammad Rabi'u da kuma Abubakar Tugga.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel